1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar ranar ma'aikata

Usman ShehuMay 1, 2014

Akalla mutane 50 suka jikkata kana aka tsare wasu kimanin 140 bayan da 'yan sanda a birnin Istanbul na kasar Turkiya suka yi arangama da masu bore

https://p.dw.com/p/1Bs3a
Istanbul Türkei Proteste Demonstration 1. Mai
Hoto: Reuters

Masu boren suna adawa ne da shirin gwamnati na gina kasuwar zamani a birnin, inda suka nemi kutsawa wajen dandalin shakatawa da aka sani da Taksim, wanda gwamnatin ke son turewa domin gina sabuwar kasuwa. A bara ma dai dubban jama'a ne suka yi kwanaki suna boren adawa da shirin gwamnati na sare bishiyoy a wajen shakatawan, domin yin sabbin gine-gine. 'Yan sanda sun yi ta cillawa wadanda ke zanga-zangar hayaki mai sa kolla, yayinda su kuwa masu zanga-zangar ke amfani da duwatsu da wasu tarkashen, domin jifan 'yan sandan. Tun da farko dai 'yan sanda sun tushe hanyoyin birnin da dama, inda suke yi wa duk wata hanya da ke zuwa dandalin da aka sani da Taksim gawanya. Koda baki masu bude ido an haramta musu shigewa. Gwamnatin Firaminista Raccip Erdogan na daukar masu boren a matsayin 'yan ta'adda.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu