1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin lalata da mata a kamfanin Google.

Gazali Abdou Tasawa
October 26, 2018

Wata muhawara ta barke a game da zargin da ake yi wa kamfanin Google na amfani da kudi wajen boye batun cin zarafin mata da wasu shugabannin kamfanin suka yi ta hanyar tilasta masu yin lalata da su.

https://p.dw.com/p/37EJm
Google CEO Sundar Pichai
Hoto: picture-alliance/San Diego Union-Tribune/TNS/J. Gibbins

Wata muhawara ta barke a game da zargin da ake yi wa kamfanin matambayi ba ya bata na Google kan batun wani cin zarafin mata da ake zargin wasu ma'aikatan kamfanin da suka hada da wasu shugabanninsa sun aikata a shekaru biyu da suka gabata da amma kamfanin ya boye batun ta hanyar shafe bakin ma'aikatan da dama da mai ta hanyar raba masu miliyoyin Dala. 

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito a wannan Alhams babban daraktan kamfanin na Google Sundar Pichai na cewa sun sallami wasu ma'aikata 48 da suka hada da wasu manyan jami'ai kamfanin 13 a bisa laifin cin zarafin mata.

Jaridar New York Time ce dai ta fara bankado wannan labari na kokarin da kamfanin na Google ya yi na boye batun cin zarafin matan wadanda wasu daga cikin shugabannin kamfanin suka tilasta masu yin lalata da su, daga ciki har da Andy Rubin makirkirin manahajar wayar salula sanfarin Android wanda kamfanin ya tilasta masa barin kamfanin ta hanyar ba shi kudin sallama miliyan 90 na dalar Amirka domin kare mutuncin kamfanin da kokarin rufe maganar.