1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin juna tsakanin Amirka da Pakistan

Zulaiha Abubakar
January 2, 2018

Shugaba Donald Trump ya bayyana Pakistan da yin karya da yaudara kan batun yaki da ta'addanci a shafinsa na Twitter.

https://p.dw.com/p/2qEDm
USA Trump droht Pakistan via Trwitter mit Zahlungsstopp
Hoto: Reuters/J. Ernst

Shugaba Donald Trump na kasar Amirka ya soki mahukuntan kasar Pakistan da yin karya da kuma yaudara akan batun magance harkokin ta'addanci a kasar, inda ya yi  barazanar janye agaji ga kasar ta Pakistan, Trump ya kuma bayyana hakan ne a shafin sa na Twitter.

A nata bangaren kasar Pakistan ta yi sammacin jakadan kasar Amirka, a wani kokarin mayar da raddi kan batun da Tump ya yi akan danganta hukumomin Pakistan da marawa ta'addanci baya. Sai dai kakakin ofishin jakadancin Amirka, ya kara da cewar mahukuntan kasar ta Pakistan sun nemi Ambasada David Hale, ya je ma'aikatar harkokin wajen Pakistan jim kadan bayan sun mayar da martani akan zargin da Trump ya yi musu na bai wa 'yan ta'adda mafaka.

A baya dai kasar Amirka ta bai wa Pakistan gudumawar kudi har Dala Miliyan dubu 33, a matsayin tallafin agaji a shekaru 15 da suka gabata. Yayin da a wani cigaban kuma ministan harkokin wajen kasar ta Pakistan Khawaja Asif ya bayyana cewar akwai banbanci tsakanin gaskiya da saci fadi a kan lamarin.