1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin kasashen yammacin duniya da nuna halin ko-oho ga rikicin Masar

August 20, 2013

Bangarorin da ke fito na fito a Masar, sun cimma daidaito wajen nuna fushinsu ga manufofin kasashen yammacin duniya game da rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/19Tgd
Aug. 17, 2013 - Cairo, Egypt - Egyptians security forces escort an Islamist supporter of the Muslim Brotherhood out of the al-Fatah mosque through angry crowds, in downtown Cairo, Egypt, on August 17, 2013...Photo: Mohamed Mahmoud/NurPhoto
Hoto: picture alliance ZUMAPRESS.com

Kungiyar 'yan uwa Musulmi a kasar Masar dai na zargin gwamnatin shugaba Obama na kasar Amirka da nuna goyon baya ga juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Mohammed Mursi, domin a cewar wani jigo a jam'iyyar Freeedom and Justice Party ta 'yan uwa Musulmi Essam el-Erian, Obama ya fito fili yayi barazanar sanya musu takunkumin karya tattalin arziki.

Sai dai bangaren da ke adawa da kungiyar 'yan uwa Musulmi irin jaridar al-Youm al-Sabi da a ke bugawa a Masar, ta yi anfani da kakausar lafazi wajen yin suka ga manufofin Obama, bisa abin da tace goyon bayan da ya baiwa kungiyar 'yan uwa Musulmi domin tabbatar da muradun Amirka a kasar ta Masar. Jaridar ta kara da cewar, yayi hakanne domin a zatonsa sabanin haka, karan tsaye ne ga yakin da a cikinsa gwamnatinsa ta zuba jari na miliyoyin kudin dalar Amirka.

Kasashen yamma na cikin tsaka mai wuya ga rikicin Masar

A bisa wadannan zarge-zarge ne, Gamal Sultan, masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Amirka da ke birnin alQahiran Masar, ya ce dukkan bangarorin biyu na yin Allah wadai da matsayin da kasashen yammacin duniya irin Amirka da ma na kasashen Turai irinsu Italiya da Jamus ke dauka a kan rikicin na Masar, na rashin nuna goyon baya a garesu:

Ya ce "Gwamnatin Masar na ganin cewar kasashen yammacin duniya ba sa basu gudummowar da ta dace wajen yaki da abin da suke fassarawa da yaki da ta'addanci, yayinda kungiyar 'yan uwa Musulmi kuwa ke fassara batun a matsayin juyin mulki ne ga zababbiyar gwamnatin dimokradiyya, kuma tana takaicin yadda kasashen yammacin duniya ke nuna halin ko oho dangane da batun kare manufofin dimokradiyya da 'yancin bil'Adama."

A cewar masanin, dukkan bangarorin biyu na ganin suna wakiltar manufofin da kasashen yammacin duniya ke da'awar karewa, amma kuma a yanzu suka ki mutunta kokarin da sassan ke yi na ganin manufofin sun tabbata.

Ribar da ke cikin hulda tsakanin Masar da kasashen yamma

Ko da shike anan Turai ma masana na da ra'ayin cewar, bagarorin da ke rikici a kasar ta Masar na nuna takaicinsu ga abin da suke ganin rashin samun goyon bayan kasashen yammacin duniya, amma suna bayyana fatan cewar, sannu a hankali za su sassauto saboda alfanun da ke tattare da kawancen da Masar din ke da shi da kasashen na yammacin duniya.

Klaus Brandner, dan majalisar dokokin Jamus daga jam'iyyar SPD, kana shugaban hadin gwiwa na 'yan majalisun dokokin Jamus da Masar, ya ce hatsari ne a sami koma baya ga kyakkyawar alakar da ke tsakanin Masar da kasashen na yammacin duniya:

Ya ce "Hatta Yan bokon Masar ma sun kwana da sanin cewar akwai alfanun da ke tattare da dabi'u da manufofin kasashen yammacin duniya, nasarorin kuwa sun hada da na tattalin arziki da kare 'yancin bil'Adama, da kuma 'yancin walwala, da kuma baiwa kowa da kowa 'yancin samun ilimi mai inganci."

Ya zuwa yanzu dai masanan na ganin cewar, kasashen na yammacin duniya na cikin tsaka mai wuya ne dangane da rikicin na Masar, domin duk wani furuci ko kuma matakin da suka dauka, a kan bangare guda, to, kuwa daya bangaren zai zargesu da nuna son kai ne.

Mawallafi : Knipp, Kersten / Saleh Umar Saleh

Edita : Mouhamadou Awal Balarabe