1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin magudi a zaben Gini

Pinado Abdu WabaOctober 12, 2015

'Yan adawa ne ke wannan zargi, kuma daga cikin hujjojin da suka bayar har da cewa wasu yankuna ba su sami katin zabe ba.

https://p.dw.com/p/1Gmwf
Präsidentenwahl Guinea Alpha Condé
Hoto: DW/B. Barry

Duk 'yan adawan da suka tsaya takarar neman shugabancin kasar Guinea, su bakwai, wadanda kuma suka kalubalanci shugaba mai ci Alpha Conde sun yi kira da a soke zaben bisa zargin tabka magudi.

Wannan furuci na su ka iya janyo fargaba a wannan kasar da ta yi kaurin suna wajen rikicin bayan zabe musamman irin na kabilanci.

Conde wanda ya hau karagar mulki bayan juyin mulki, ya sami magoya baya sosai a zaben ranar lahadi sai dai wata kila ratan da ya ba abokan hammayarsa ba zai yi tazarar sosai ba ta yadda sai an je zagaye na biyu a zaben.

'Yan adawan dai a karkashin jagorancin madugun su Cellou Dalein Diallo sun fadawa wani taron manema labarai cewa akwai magudi da kura-kurai da dama, inda ya kwatanta cewa, akwai yankunan da basu ma sami katin zabe ba duk da cewa an yi musu rajista