1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin sarrafa wa dabbobi abincin 'yan gudun hijira

Abdullahi Maidawa Kurgwi
August 4, 2017

Jami'an tsaro a Jihar Filato da ke Najeriya na ci gaba da bincike don gano yadda aka karkatar da hatsi da aka tanadarwa 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2hioT
Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Jami'an tsaro a Jihar Filato na ci gaba da bincike don gano yadda aka karkatar da wani hatsi da aka tanadar don 'yan gudun hijira, wannan na zuwa ne bayan an bankado tarin hatsin a kamfanin sarrafa abinci na Grand Cereal da ke birnin Jos, jami’an tsaron sun bankado yadda kanfanin ya tara wannan hatsi a rumbunsa na tara abinci da a ke anfani da shi wajen sarrafa abincin dabbobi, kwamishanan 'yan sandan jihar shi da kansa ya je kanfanin tare da wani ayarin jami’an tsaro don kaddamar da bincike, sun kuma gano tarin buhuhunan hatsi a kamfanin.Bayan tuntubar hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA shiyyar Arewa maso Tsakiya, don sanin gaskiyar al'amarin ko shin hukumar na da wata masaniya kan wannan abinci da aka gano, amman kakakin hukumar ya ce sam babu wadannan kayayyakin abincin da ake cece-ku-ce a kai.     

Malawi World Food Programme
Hoto: picture-alliance/dpa/dpaweb/J. Hrusa

Wani jami’in kanfanin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya sheda cewar wani dan kwangila ne da kanfanin ya ba shi kwantiragin sayo masara, shi ne ya zuba masarar da ya sayo a cikin mazubi mai dauke da rubutu ''Abincin tallafi na gwamnatin tarayya'' Yanzu dai lokaci ne kadai zai nuna gaskiyar wannan lamari, kasancewar kwamishinan 'yan sandan jihar Filato da kansa ya kaddamar da bincike tun farko don gano yadda aka yi kamfanin na Grand Cereal ya sami wannan hatsi mai tarin yawa yana sarrafa abincin dabbobi da shi.Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da gwamnatin Najeriya da wasu kasashen waje irin su Saudiyya ke bayar da tallafi saboda amfanin 'yan gudun hijira amma akan karkarta da akalar agajin.