1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabwe ta yi barazanar fita daga SADC

July 5, 2013

Bayan da kotu ta yi watsi da bukatar dage zabuka a Zimbabawe kamar yadda kungiyar SADC ta nema, Mugabe ya gargadi SADC din da ta daina yi masa shisshigi.

https://p.dw.com/p/192wF
Hoto: AP

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya kaddamar da gangamin yakin neman zabensa, biyo bayan hukuncin ta kotun tsarin mulkin kasar ta yanke na gudanar da zabukan kasar ranar 31 ga wannan wata na Yuli da muke ciki.

Tun da farko dai Mugabe ya nemi a dage ranar zaben da makwanni biyu bayan da kungiyar hadin kan kasashen kudancin Afirka SADC ta bukaci ya yi hakan, sakamakon korafin da 'yan adawa suka yi na shakku kan gudanar da zabe mai inganci a kurataccen lokaci, sai dai kotu ta yi watsi da wannan bukata ta Mugabe.

A yayin kaddamar da gangamin yakin neman zaben nasa, Mugabe ya yi barazanar ficewa daga cikin kungiyar SADC in har ta nemi ta sake yin katsalandan a al'amuran kasar sa, ya na mai cewa dama sun shiga kungiyar ne domin radin kansu kuma a shirye suke su fice daga cikin ta.

Mugabe ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su jajirce domin tabbatar da ganin sun yi nasara a zabukan da za a gudanar a Zimbabwen, wanda in har ya lashe zaben zai bashi damar dorawa a kan shekaru 33 da ya kwashe yana kan karagar mulkin kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe