1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zirin Gaza na cikin kaduwa tun bayan juyin mulki a Masar

August 23, 2013

Juyin mulkin da aka yi a Masar ya matukar shafar makwabciyarta Zirin Gaza, inda yanzu daruruwan mutane ba sa iya fita daga yankin domin an rufe kan iyakarsa da Masar.

https://p.dw.com/p/19VRK
ARCHIV - Ägyptische Soldaten bewachen am 04.06.2012 den gesperrten Grenzübergang in Rafah zwischen dem Gazastreifen und der ägyptischen Sinai-Halbionsel. Nach dem verheerenden Anschlag auf einen Militärkontrollposten auf der Halbinsel Sinai suchen die ägyptischen Sicherheitskräfte nach weiteren Attentätern, die die Aktion überlebt haben könnten. Bei dem Anschlag am Vorabend waren 16 ägyptische Soldaten getötet worden. EPA/ALI ALI dpa (zu dpa 0284 am 06.08.2012) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Hatta sumogar kayakin masarufi ta hanyoyin karkashin kasa a kudancin yankin na gamuwa da cikas. Kungiyar Hamas dake mulki a yankin ta dora fatanta a kan gwamnatin 'Yan uwa Musulmi, a yanzu dole ta canja tunani.

Tun bayan juyin mulkin da aka yi a Masar, ba a bude kan iyakar Zirin Gaza da Masar, in ma an bude bai wuce sa'o'i kalilan a rana ba. Nabil El Shurafa mai ejan ne a garin Gaza, abin da ya fi yi a yanzu shi ne soke tikitin matafiya ta jirgin sama ko canja musu lokacin tafiya.

Mazauna Gaza sun fi jin jiki

"A duk lokacin da aka samu matsala a yankin mazauna Gaza sun fi ji a jika. Aikinmu a wannan ofis na ejan shine sayar da tikitin tafiya da tsara lokacin tafiyar ko soke shi gaba daya kuma muna kokarin ganin matafiyan ba su biya kudi da yawa ba."

Gaza Streifen Nabil Shurafa muss Tickets stornieren Bild: DW/Tania Krämer, DWTV
A kullum Nabil Shurafa na soke tikitin matafiyaHoto: DW/T. Krämer

Tafiyar da wani kamfanin ejan a wani yanki da akasarin mazaunansa miliyan 1.7 ba sa iya fita lokacin da suka so, abu ne mai wahalar gaske musamman a kwanakin nan. Ko a wasu watannin bayan nan kafin hambarar da gwamnatin Mohammed Mursi ketarawa ta kan iyakar Gaza a Rafah wani abu ne mai bukatar hakuri sosai. Matafiya na cikin takaici da rashin sanin tabbas a zauren zaman jiran samun izinin ficewa. Wasu na zuwa a kullum domin gwajin sa'a, kamar wannan matashi dalibi dake karatu a kasar Aljeriya.

"Ina da wata muhimmiyar jarrabawa da zan yi a ranar daya ga watan Satumba kuma izinin shiga kasar zai kare a ranar uku ga watan Satumba. Tun mako guda da ya wuce nake kai komo a nan don ficewa. Ba Gaza ce kadai ke da iyaka da Masar ba, amma ana rufe kan iyakar a kullum. Mu ma 'yan Adam ne ba dabbobi ba."

Gaza Streifen Kleine Protestaktion am Grenzübergang Rafah gegen die schwierigen Ausreisebedingungen Bild: DW/Tania Krämer, DWTV
Karamar zanga-zanga a kan iyakar RafahHoto: DW/T. Krämer

Wannan matashi da sauran matafiya sun yi zanga-zanga dauke da kwalaye domin jawo hankali game da mawuyaci halin da suke ciki, amma ba wanda ya nuna sha'awa ga wannan boren, domin ba wani jami'i a wurin da zai taimake su. Su kansu hukumomin Hamas ba sa a wurin domin su kansu tasu ta ishe su. Sauyin mulki da aka samu a Masar ta girgizar Hamas wadda ke mulki a Zirin Gaza tun shekarar 2007, inji Omar Shaban manazarcin harkokin siyasar Falasdinu.

"Abin da ya faru a Masar tamkar wata Tsunami ce ta siyasa da tattalin arziki ga Hamas. Kungiyar 'Yan uwa Musulmi da ta yi mulki a Masar tsawon shekara guda ta ba wa Hamas taimako na siyasa, tattalin arziki hade da wani kwarin guiwa."

Juyin mulki a Masar ya dagula wa Hamas lissafi

Ya zuwa wannan lokaci kusan komi na tafiya da kyau ga gwamnatin Hamas domin kungiyar 'Yan uwa Musulmi ta zama mata wata kawa mai muhimmanci. Sannan Qatar ta yi alkawarin ba da taimakon kudi na miliyoyin dala, sai dai sauyin mulki na ba zata zai sa dole Hamas ta canja tunani.

Masharhanta na ganin na gaba kadan zai zame wa Hamas dole ta dauki tsauraran matakai domin tabbatar da ikonta a wannan karamin yanki. Sai dai ita ma ta san dole ta yi takatsantsa don kaucewa fushin sabbin mahukuntan Masar.

Mawallafa: Tania Krämer / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe