1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Koffi Annan a Afrika ta Kudu

March 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv53

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan ya kai ziyara aiki a Afrika ta kudu, inda ya tantanan da shugaba Tabon Mbeki, a game da batutuwan da su ka shafi rayuwar Afrika, mussaman ta fannin cigaba, da riginginmun da wannan nahiyar ke fuskanta.

Annan, ya yi yabo ga rawar da Afrika ta kudu ke takawa wajen warware rigingimun na Afrika, da kuma yadda wannan ƙasa ta hau turba ci gaba.

Gobe ne idan Allah ya kai mu Koffi annan ke ganawa da tsofan shugaban ƙasa Nelson Madella. Sannan ya zarce zuwa ƙasar Madagascar, da Kongo, inda zai gana da shugaban taraya Afrika, Dennis Sassun Nguesso.

Zai kammala wannan ziyara da Jamhuriya Demokaraɗiyar Congo.

A ƙarshen shekara da mu ke ciki, Koffi Annan zai kai ƙarshen wa´ adin mukamin sa, na sakatare Jannar a Majalisar Ɗindin Dunia.