1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

041208 EU Tibet

Mohammad AwalDecember 4, 2008

A yau Alhamis shugaban addinin yankin Tibet Dalai Lama zai yi wani jawabi a gaban majalisar dokokin Turai dake birnin Brussels.

https://p.dw.com/p/G8yr
Dalai Lama lokacin ziyararsa Berlin a cikin watan MayuHoto: AP

Baya ga haka shugaban addinin na Tibet zai gana ƙeƙe da ƙeƙe da shugabannin ɓangarorin jam´iyu masu wakilci a majalisar. Don nuna adawar ta da tarbar da manyan wakilan ƙungiyar EU suka yiwa Dalai Lama gwamnatin Beijing ta soke wani taron ƙoli tsakaninta da EU da aka shirya ya gudanarwa a birnin Lyon ranar Litinin da ta gabata.

Sama da ´yan majalisar dokokin Turai 30 ne suka ƙuduri aniyar yin azumi na tsawon kwana guda wato sa´o´i 24 don nuna zumunci ga Dalai Lama da kuma yankin Tibet. Hakazalika za a kuma raba fararen kyallaye fiye da 800 ga ´yan majalisar a lokacin da shugaban na addinin yankin Tibet zai fara jawabi a gaban majalisar yau da rana.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Dalai Lama zai yiwa majalisar jawabi ba amma ziyararsa ta yau ta samu wani muhimmanci na musamman. Gabanin wasannin Olympics, hukumomi a birnin Beijing sun nuna alamun tattaunawa da ´yan Tibet amma bayan wasannin an dakatar da wannan ƙoƙari.

Majalisar Turai na ƙorafin cewa har yanzu China ta dage kan bin manufofin tursasawa al´umar yankin. Saboda haka ya zama wajibi a fito ƙarara a nuna matsayin da ake kai, inji wakiliyar jam´iyar The Greens ta ƙasar Austria Eva Lichtenberger.

"A kullum majalisar dokokin Turai ta na ba da muhimmanci ga batun kare haƙin Bil Adama wataƙila fiye da abubuwan dake wakana a cikin majalisar shawara. Amma na yi imanin cewa ba za a samu saɓani a nan ba."

Masu goyon bayan fafatukar ´yan yankin Tibet sun samun ƙarfin guiwa dangane da ganawar da za a yi a ƙarshen mako a ƙasar Poland tsakanin shugaban Faransa Nikolas Sarkozy da Dalai Lama. To sai dai China ta fusata da haka a saboda haka ta soke taron ƙolin shekara shekara tsakaninta da ƙungiyar EU, wanda hakan ke nufin wani tsamin dangantaka tsakanin EU da China. Saboda haka ake ƙara mayar da hankali ga jawabin da Dalai Lama zai yi a yau. Eva Lichtenberger ´yar jam´iyar The Greens daga Austria na mai ra´ayin cewa matakan da gwamnati a Beijing ke ɗauka ba su dace ba.

"Ko shakka babu wannan mutumin zai ba da shawarwari ne don warware wannan matsala cikin lumana amma ba sanar da wani sabon rikici ba."

A ranar Asabar dai shugaban majalisar shawara ta EU, Nikolas Sarkozy zai gana da Dalai Lama a Poland. Yayin wasannin Olympics bisa adawar da China ta nuna, Sarkozy ya ƙi ganawa da Dalai Lama lokacin da ya kai ziyara Faransa.

Tun bayan da ya tsere daga Tibet sakamakon murƙushe wani boren yankin a 1959, China na ɗaukar Dalai Lama a matsayin ɗan aware. Shi dai Dalai Lama wanda ya taɓa samun kyautar zaman lafiya ta Nobel yana goyon bayan bawa yankin Tibet ƙarin ´yancin cin gashin kai amma ba mulkin kai kamar yadda China ke zarginsa ba.