1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Keita a yankin arewacin Mali

March 19, 2014

Wannan ziyara da ta shiga rana ta uku, ita ce ta farko tun bayan zaben Ibrahim Boubakar Keita a matsayin shugaban kasa a watan August na shekara ta 2013.

https://p.dw.com/p/1BSBE
Ibrahim Boubacar Keita Präsident Mali
Hoto: Reuters

Shugaban na kasar Mali ya fara ziyartar arewacin kasar ne da garin Sevare, da ke a nisan km 600 a arewa maso gabashin Bamako babban birnin kasar,inda nan take ya fara da ziyartar dakarun sojan kasar ta Mali da ke da wata cibiya a wannan gari.

A cikin wannan rangadi ne, Shugaban kasar ta Mali Ibrahim Boubakar keita, zai jagorancin bukin kaddamar da wani sabon babban asibiti, da kuma wasu sabin cibiyoyin samar da wutar lantarki guda biyu da aka same su ta hanyar Bankin Duniya.

Sai dai duk da iri-irin wadan nan ababan mora rayuwa da aka fara samu, akwai manya-manyan matsaloli dangane da batun sasantawa da juna tsanakin al'ummar wannan yanki, kamar yadda Cheikna Niang, shugaban tsarin dake tallafawa kungiyoyin fafaran hula na jihar Mopti ke cewa;

"Tsarin sasantawa da juna abu ne da ke tafiyar hawainiya a wannan yanki idan aka yi la'akkari da kura-kuran da aka tafka, wadanda suka haifar da rarrabuwar kawun tsakanin al'umma, dan haka sake dawowa a sasanta, abu ne da zai dauki lokaci mai tsawo domin sai da wayar da kawunan mutane kan batu yafiya, ta yadda su kansu mutanen zasu yarda su yafe ma juna, dan a samu dawowa cikin kyaukyawan yanayi, amma kuma yanzu ana iya cewa abun dai ya fara tafiya sannu a hankali, mutane sun fara magana da juna, wasu sun fara hulda da juna, kuma dari-darin da da mutane keyi wa junan su, yanzu ya fara sauki."

Im Vorfeld der Parlamentswahlen in Mali
Babban titi a cikin kasar MaliHoto: Getty Images/Afp/Issouf Sanogo

Ko yaya batun ma'aikatu daban-daban na gwamnati suke a wannan yanki, ko ana iya cewa duk komai ya fara tafiya daidai ta yadda kowa ke aikin sa, sai Cheikna Niang yaci gaba da cewa

"A'a ba haka ba domin koi ma'aikatu sun buda ne kawai a babban birnin jiha wato Mopti, kuma bisa abun da ya shafi fannin tsaro shima muna iya cewa har yanzu dakwai sauran rina a kaba, domin yan tawaye, ko kuma nace Buzayen da gwwamnati ta dauka ta sa cikin fanni daban daban na jamiyan tsaro, ganin cewa sun san lungu-lungu sako-sako na arewacin wannan kasa, sune kuma ke dawowa a matsayin yan ta'adda suna sace-sacen mutane da ma kwasar ganima."

Ganin cewa shugaban kasar ta Mali na ziyarar sa ta farko ce a arewacin kasar, ko mi su suke jira dangane da wannan ziyara tashi.Cheikna Niang shugaban tsarin da ke tallafa wa kungiyoyin fafaren hula na jihar Mopti ya ci gaba da cewa;

"Muna jira daga shugaban kasa wani kokari bisa batun farfado da tattalin arzikin wannan jiha, ganin yadda rikicin ya haifar da koma bayan tattalin arzikin al'umma, da ma batun makamashi na wutar lantarki da yake wata babbar matsala a halin yanzu, wannan jiha na jiran gani daga shugaban kasa yadda zai yi kokarin samar da wasu kayayakin da al'ummar wannan jiha ta rasa sakamakon rikicin, da farfado da sauran ma'aikatun kula da jin dadin al'umma domin bawai dadin baki na siyasa ba ne ake so, aa, ana so ne a gani zahiri a kasa."

Im Vorfeld der Parlamentswahlen in Mali
Mata a yankin arewacin MaliHoto: picture-alliance/AP

Jihar Mopti dai, ta kasance a yankin karshe na arewacin kasar ta Mali, yanki mai fadin gaske, da ya samu mamayar kungiyoyi masu kishin Islama dake da alaka da kungiyar Al-Ka'ida, tsawon watanni goma, daga shekara ta 2012 zuwa 2013 wadanda aka kora sakamakon matakin soja na dakarun kasa da kasa da suka kawo wa wannan kasa ta Mali dauki a watan Janeru na 2013 bisa fusa'ar kasar Faransa da har yanzu ke ci gaba da gudana a wannan kasa.

Mawallafi : Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohammed Abubakar