1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR SCHÖDER A NAHIYAR AFRIKA

ZAINAB AM ABUBAKARJanuary 21, 2004
https://p.dw.com/p/BvmR
Shugaban gwamnatin Jamus Gehard Schroder,acigaba da rangadin aiki dayakeyi a wasu kasashen Afrika ya yabawa sabuwar gwamnatin Kenya,inda a sakamakon hakane ya sanar da ninka agajin daya shirya bawa Kenya,domin taimakawa kasar inganta Democradiyyanta ,bayan ta kasance karkashin mulkin kama karya na shekaru masu yawa. Shugaba Schroder bayan ganawarsa da Shugaba Mwai Kibaki na Kenya,yace zaa ninka tallfi da Jamus zata bawa kasar zuwa Euro million 25,kwatankwacin dalan Amurka million 31 da digo 74 kenan,akowace shekara dada wannan shekarata 2004 da kuma shekarata 2005,kana Jamus zata taimakawa Kenya yaki da ayyukan taaddanci. Shugaban na jamus wanda ya bayyana democradiyyan Kenya a matsayin zakaran gwajin dafi wa sauran kasashen nahiyar,yace Kenya babbar Abokiyar huldan Jamus ce a wannan yanki nasu.
Ziyaran na Shugaban na gwamnatin Jamus na mai zaman na farkon irinsa a bangaren shugabannin nahiyar Turai cikin watanni 12 da suka gabata,Shekara guda da yan Kai kenan da kasar ta Kenya ta samu daman kafa gwamnatin democradiyya,bayan tsohon shugaba Daniel Arap Moi yayi murabus daga shugabancin kasar. Idan zaa iya tunawa shugaba George W Bush na Amurka ya kai ziyara a nahiyar a shekarar data gabata amma,bai je Kenya ba duk da ikirarinsa na goyon bayan democradiyya.
Manazarta sun bayyana cewa an fuskanci matsaloli na rashawa tsakanin yan kasuwa da manyan jamian gwamnati,akarshin mulkin kama karya na tsohon shugaba Moi na tsawon shekaru 24 a Kenya.A yanzu haka dai shugaba Mwai Kibaki ya mike tsaye wajen yaki da rashawa ,kana yana kokarin gano dala billion 4 na gwamnati ,da jamian baya suka sata kana suka boye a asusun kasashen waje.
Schroder ya isa Kenyan ne jiya,bayan ziyararsa ta farko a Ethiopia,ziyarar da zata kaishi Afrika ta kudu,da Ghana,inda kuma zai tattauna batutuwan tallafi,cinikayya da tsaro.Jamian Diplomasiyya anan Jamus sun sanar dacewa an zabi wadannan kasashe ne domin suna masu zama abun alfahari a zaman lafiya a Afrika ,kana harkokin democradiyya da suke ciki a halin yanzu yana mai zama abun koyi ga sauran kasashen dake ikirarin cewa suna democradiyya. Schroder ya kumayi amfani da wannan dama wajen yabawa kenya,a matsayinta mai masaukin baki na warware rikicin kasashen Sudan da Somalia.Bugu da kari yace Jamus a shirye take ta shiga dukkan harkokin tallafi na kasa da kasa. Dayake amsa tambayoyin manema labaru bayan ganawarsa da manyan jamian lura da shirin kula da Muhalli na Mdd dake da headquater a Nairobi,Klaus Toepfer da Ann Tibaijuka,shugaba Schroder yace matsayin Jamus ya canja a duniya,tun bayan hadewan gabashi da yammacin kasar a shekara ta 1990.Adangane da hakane kasar zata sauke kowane hakki daya rataya a wuyanta na tallafawa kasashen duniya.Inda yace Jamus ta taka rawar gani a rikicin yankin Balkans da Afganistan,bayan hambare gwamnatin yan Taliban a shekarata 2002.Bugu da kari duk da adawa da yakin daya hambare gwamnatin Sadam Hussein a Iraki,a yanzu haka Jamus na laakari da horar da Yansandan binciken miyagun ayyuka na kasar ta Iraki.
Wannan ziyara na mai zama irinsa na farko da Shugaban gwamnatin Jamus din yakai nahiyar Afrika,tunda ya haye mulki a shekarata 1998,wanda kuma keda nufin inganta dangantaka tsakanin kasashen kasashen tare da taimakawa harkokin tsaro.