1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zuma zai jagorancin ANC a zaben shekarar 2014

December 21, 2012

Babban taron jam'iyar ANC karo na 53 ya tabbatar da Jacob Zuma a mukamin shugaban jam'iyar na sabon wa'adin shekaru biyar.

https://p.dw.com/p/177TT
Hoto: Stephane de Sakutin/AFP/Getty Images

Bari mu fara da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda a babban labarinta a wannan mako ta yi tsokaci a kan sake zaben shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma a mukamin shugaban jam'iyar ANC mai mulki a kasar. Jaridar ta ce kamar yadda aka yi zato babban taron ANC karo na 53 ya tabbatar da Jacob Zuma a mukamin shugaban jam'iyar na sabon wa'adin shekaru biyar, wanda haka kuma ya sanya shi zama ɗan takararta a zaben 'yan majalisar dokoki a shekarar 2014. An kuma zabi hanshakin dan kasuwa Cyril Ramaphosa a matsayin mataimakinsa, wanda ya maye gurbin Kgalema Motlanthe mutumin da ya kalubalanci shugaba Zuma. Sai dai babban taron na ANC da ya gudana a Bloemfontein, ya ci karo da tashe tashen hankula tsakanin bangarori da suka zargin juna da tabka magudi wajen zaben wakilai da kuma sauya sakamakon zaben.

'Yan Somaliya sun shiga uku a Kenya

Kenya ta haramta wa 'yan gudun hijirar Somaliya zama a cikin biranen kasar, inji jaridar Süddeutsche Zeitung, sannan sai ta ci gaba da cewa. Sun tsere daga yaki da yunwa a Somaliya ga shi yanzu an ayyanasu a matsayin barazana ga kasar da ta ba su mafaka.

Gwamnatin Kenya ta ba da umarnin cewa, dukkan 'yan gudun hijirar Somaliya sun fice daga biranen kasar, su koma sansanonin 'yan gudun hijira. Wannan matakin inji jaridar ya shafi mutane fiye da dubu 30 a birnin Nairobi kadai. A makonnin baya bayan nan an yi ta samun fashewar bama-bamai a Nairobi, musamman a unguwannin 'yan Somaliya. Akalla mutane 13 sun rasu sannan da dama sun samu raunuka. Ko da yake har yanzu ba a gano wadanda suka aikata ta'asar ba, amma ana zargin mayakan kungiyar al-Shabaab da hannu. Kungiyar wadda ta shafe lokaci mai tsawo tana iko da wasu yankunan Somaliya, a watannin baya bayan, dakarun Kenya dake aiki karkashin inuwar kungiyar tarayyar Afirka sun fatattaki sojojin sa kai na al-Shabaab daga tungarsu. Al-Shabaab ta yi barazanar daukar fansa a kan Kenya.

Bombenanschlag Kenia Nairobi 7.12.2012
Ana zargin 'yan Somaliya da laifin fashewar bama-bamai a NairobiHoto: AP

'Yan tawayen Hutu sun fara kai hari cikin Ruwanda

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung labari ta buga game da sojojin sa kai na kabilar Hutu, da ta ce sun fara kaddamar da yaki a kasarsu. Ta ce a karon farko cikin shekaru da yawa, kungiyar 'yan tawayen FDLR dake zaune a Kongo, sun kai farmaki a kan yankin kasar Ruwanda, kuma soojojin sa kai sun ce yanzu aka fara. Jaridar ta rawaito majiyoyin leken asirin Ruwanda na cewa 'yan tawayen na kungiyar FDLR ta girke daruruwan mayaka a wani yanki dake kusan da kan iyakar Ruwanda, inda daga nan suke kai hari cikin kasar. Kungiyar ta yi amfani da rikicin gabacin Kongo tsakanin sojoji da 'yan tawayen kungiyar M23, don kutsawa cikin Ruwanda.

Kongo - FDLR Kämpfer kontrollieren Kalembe
'Yan tawayen FDLR su fara kaddamar da hari cikin RuwandaHoto: DW

China a harkar watsa labaru a Afirka

Kasar Sin ta shiga gadan-gadan cikin harkar watsa labaru a Afirka, inda yanzu haka ake buga wata jaridar mako mako ta China Daily a babban birnin kasar Kenya, Nairobi, inji jaridar Berliner Zeitung. Jaridar ta ce ba tababa China ta samu karbuwa a Afirka, kuma nan gaba kadan za ta kasance abokiyar hulda ciniki mafi girma ga nahiyar Afirka, wadda Turawan mulkin mallaka suka jima suna hulda da ita. Daga shekarar 2000 zuwa yau ciniki tsakanin Afirka da China ya ninka fiye da sau ashirin, yayin da nahiyar Turai da Amirka suka rasa babban kaso na harkar kasuwanci da wannan nahiya dake samun bunkasar tattalin arziki.

MawallafI: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi