1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afrika ta yamma na neman hana cinikin makamai

May 26, 2014

kungiyar raya tattalin arzikin yammcin Afrika ECOWAS ko CEDEAO ta karfafa sabbin dubarun shawo kan matsalar yaduwar makamai, wacce ta jefa yankin cikin mawuyacin hali na bullar ayyukan ta’addanci.

https://p.dw.com/p/1C7Hp
Hoto: Reuters

Wadannan sabbin dubaru da kungiyar ta Ecowas ta dauka, ya biyo bayan sabon salon da matsalar watsuwar kanana makamai ke yi a yankin Afrika ta yamma. Tuni ma a zahiri ake ganin illar matsalar saboda ruruwar da tashe-tashen hankula ke yi da kuma aiyyukan ta'adanci da ke neman gindin zama kama daga kasar Mali zuwa Najeriya da Jamhuriyar Nijar har ma da kamaru.

Abin da yafi daga hankalin kungiyar shi ne yadda yawan kanana makaman da aka kiyasata na hannun jama'a a Afrika ta yamma sun kai milyan takwas. Sannan ma barazanar da suke haifarwa ya sanya bullo da yarjejeniyar cinikin makamai a karakashin Majalisar Dinkin Dunioya a 2013, bisa fatan zata taimaka shawo kan matsalar.

Hajiya Salamatu Sulaiman, kwaminiyar zaman lafiya, tsaro da siyasa ta kungiyar Ecowas ta ce " abin da ke faruwa a Najeriya in an ciwo kansu, mai yiwuwa ne a samu zaman lafiya da ci gaban demokaradiyya da sauran abubuwan da ya kamata a samu a yanzu. Wannan ya sa ake bullo da wadannan dubaru."

Nigerdelta Angriff Rebellen
Ana amfani da makamai wajen fasa bututuyan mai a yankin Niger DeltaHoto: picture alliance/dpa

Kwarraru a taron na Abuja sun nuna damuwa a kan jan kafar da ake fuskanta wajen samun kasasheda za su sanya hannu a kan yarjejeniyar da za ta taimaka sa ido a kan cinikin makamai a tsarin da ka iya dakile shigarsu a hannun jama'a. Sai dai daga cikin kasashen duniya 32 da suka amince da ita, Najeriya da Mali ne kadai daga yankin Afrika ta yamma.

Babban sakatare a ma'aikatar kula da harkokin kasashen wajen Najeriya Mr Martins Umoh ya ce " matsalar ta'adanci tafi ta'azarra kama daga Alqaeda zuwa Alshabab duka suna a nahiyar nan, kuma ta hanyar kanana makamai ne suke kai hare-harensu , don wannan nahiyar ce ya kamata ta zama kan gaba wajen sanya hannu a wannan yarjejeniya''.

Liberia Kindersoldatin mit Waffe
Yara ma na amfani da makamai a fagen yakiHoto: Getty Images

Kwararru sun bayyana cewa kasashen da ke kera makaman ne ya dace a matsa wa lamba wajen ganin sun sanya hannu a kan yarjejeniyar, muddin ana fatan samun tasirinta.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe