1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci gwamnatin Tarayya ta karfafa matakan tsaro

Mohammad AwalFebruary 24, 2014

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Tarayyar Najeriya ta nemi gwamnatin kasar ta kara himma wajen tura jami'an tsaro da isassun kayan yaki, domin kawo karshen zubar da jinin al'umma a yankin.

https://p.dw.com/p/1BEgm
Bildergalerie Kriege im Jahr 2013
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan kira na tura karin sojoji da kayan aiki na kunshe ne a wani martani da kungiyar gwamnonin ta fitar domin nuna alhini ga kisan fararen hula da aka yi a karshen makon nan a wasu sassan jihohin arewacin kasar.

Shugaban kungiyar wanda kuma shi ne gwamnan Jihar Neja Mu'azu Babangida Aliyu ya bayyana a sanarwar cewa daukacin gwamnonin yankin sun damu matuka da yadda ake samun kashe-kashe yawanci na fararen hula da ba su san hawa bare sauka. Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin tarayyar da ta samar da karin isassun kudade ga jihohin Borno, da Yobe, da kuma Adamawa domin kulawa da wadanda wannan rikici ya rutsa da su.

Nigeria Boko Harem Angriff in Damaturu
Hoto: picture-alliance/AP

Wannan kira yana zuwa a dai dai lokacin da gwamnatin kasar ta sanar da rufe wasu iyakokin kasar da Kamaru a wani mataki na magance hare-hare da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram. Sai dai wasu al'ummar yankin ba sa goyon bayan matakin kara tura sojoji da makamai zuwa wannan yankin maimakon haka kamata ya yi gwamnatin ta samo hanyar laluma domin kawo karshen zubar da jini a yankin.

Malam Adamu Adamu Maidala mai fashin baki kan harkokin yau da kullum na cikin masu irin wannan na gwamnati ta nemo hanyar yin sulhu da 'yan rungiyar.
Shima Dr Khalifa Dikwa wani tsohon Malamin jami'ar Maiduguri ya shaida min ta wayar tarho cewa wannan mataki na tura soja ba zai haifar da alheri ba.

Nigeria Kampf gegen Boko Haram Islamisten
Hoto: Getty Images/AFP

Ya ce "Wannan kiran sun yi shi a baya kuwa yawan soja ba zai yi maganin wannan al'amari ba saboda kullum suna sauya salon suna yakin sunkuru mafita dai kawai itac e ta siyasa ta tattaunawa."

Ganin wannan ba shi ne karo na farko da kungiyar gwamnonin ke yin irin wannan kira ba, amma babu wani sabon mataki na a zo a gani da gwamnatin tarayyar ta yi haka ya sa matasan yankin suka bukaci gwamnonin su koma jihohin domin gyara harkokin matasa ta haka ne kawai za a magance matsalar. Mustapha Musa Muhammad wanda aka fi sani Hon Pepe wani matashi ne mai irin wannan tunani.


Yanzu haka dai al'ummomin wannan yankin sun kasa kunne suna jira ko gwamnatin Tarayyar za ta amsa wannan kira musamman ganin shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai yi wata tattaunawa ta kai tsaye da kafafan yada labarai yau da dare (24/02/2014).

Mawallafi: A-Amin Suleiman Mohammed

Edita: Usman Shehu Usman