1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto mutane 24 a cikin saharar Nijar

Gazali Abdou Tasawa
June 27, 2017

A ranar lahadi sojojin Nijar sun ceto wasu 'yan cirani 24 'yan asalin kasashen Afirka ta Yamma daga cikin dajin Sahara inda masu safarar su suka yi watsi da su ba abinci ba ruwan sha kan hanyarsu ta zuwa kasar Libiya. 

https://p.dw.com/p/2fRgj
Afrika überladener LKW in der Sahara
Hoto: imago/alimdi

 

Mukaddashin gwamnati a garin Bilma na arewacin kasar Fatoumi Boudou, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mutanen da aka ceton sun sanar da cewa su 70 zuwa 75 aka dauko su a cikin motoci uku daga garin Agadez zuwa kasar Libiya. Haka nan kuma da dama daga cikinsu sun mutu kan hanya bayan da masu safarar tasu suka gudu suka bar su a tsakiyar Sahara. 

Wani gidan radiyon garin na Bilma ya sanar a jiya Litinin cewa daga baya jami'an sojin kasar ta Nijar sun sake yin nasarar tsinto gawarwakin mutane 52 a cikin dajin Saharar.