1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An fara sakin sakamakon zaben Kwango

December 23, 2023

Hukumar zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta fara sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da ke cike da cece-kuce kan sahihancin zaben da galibin 'yan takarar ke cewa zaben na cike da rashin inganci.

https://p.dw.com/p/4aWJy
Hoto: ZOHRA BENSEMRA/REUTERS

Hukumar zaben  Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta fara sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da ke cike da cece-kuce kan sahihancin zaben da galibin 'yan takarar ke korafin tafka magudi tare da bukatar a sake gudanar da zaben.

Sakamakon farko ya nuna cewa 'yan kasar mazauna kasashen ketare sun yi ruwan kuri'u ga shugaba mai ci Felix Tshisekedi , da ke sake neman wa'adi na biyu, a kasar dake da dimbin tattalin arzikin ma'adinai da galibin al'umma kasar ke fama da talauci.

A wani taron manema labarai a birnin Kinsasha, shugaban hukumar zaben kasar ta CENI, Denis Kadima, ya yi watsi da zarge-zargen 'yan takarar da ke adawa da sahihancin zaben da kuma masu sanya ido na kasa da kasa, inda ya ce za su ci gaba da sakin sauran sakamakon zaben shugaban kasar ta ta Kwango daga sassa daban-daban na kasar.