1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Jaridun Jamus: Zaben Kwango da rikicin Sudan

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
December 22, 2023

Hankulan jaridun Jamus a wannan makon sun karkata ne kan zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da rikicin Sudan da kuma rangadin aiki da ministar harkokin wajen Jamus ta kai Ruwanda.

https://p.dw.com/p/4aSMP
Zabe | Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Rikici
'Yan gudun hijira sun yi korafi kan rashin sunansu a rijistar zaben KwangoHoto: THOMAS MUKOYA/REUTERS

Cikin sharhinta jaridar Süddeutsche Zeitung mai taken "Tashe-tashen hankula da jinkiri wajen kai kaya runfunan zabe sun mamaye zabubbukan 'yan majalisa da na shugaban kasa a Kwango", ta ce 'yan adawa sun yi gargadi cewar da gan-gan ne aka haifar da wannan yamutsi a ranar zaben baya ga shirin Majalisar Dinkin Duniya na janye dakarunta na kiyaye zaman lafiya nan ba da jimawa ba. Jaridar ta ci gaba da cewa wata rumfar zaben tafi kama da filin daga, saboda yadda katunan zabe ke warwatse a kasa wasu ma a yayyage. An wargaza kujeru, an lalata na'urorin zabe da tagogi. An samu tashin hankali da safiyar Larabar da aka yi zaben tsakanin fusatattun masu kada kuri'a da 'yan sanda, a daya daga cikin rumfunan zaben.

Karin Bayani: Rikice-rikice a Afirka cikin Jaridun Jamus

Rahotanni na cewa wasu 'yan gudun hijira ba su samu sunayensu a cikin jerin wadanda za su kada kuri'a ba, lamarin da ya sa suka harzuka. Abin da ya haifar da hargitsi tsakaninsu da jami'an zaben, sai da 'yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa gun-gun masu zanga-zanga a tsakiyar birnin. Bunia shi ne babban birnin lardin Ituri, inda kashi uku na al'ummar yankin suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren 'yan bindiga. A Kwango, kusan mutane miliyan bakwai ne ke gudun hijira a cikin kasarsu musamman a yankunan da ake yaki a gabashin kasar, inda daukacin al'ummomin kauyuka suka yi ta kauracewa gidajensu tsawon shekaru. A ranar 20 ga watan Janairu ne dai za a sanar da sakamakon zaben da ta yiwu shugaba mai ci Felix Tshisekedi mai shekaru 60 da haihuwa zai samu nasarar zarcewa, saboda rashin hadin kan 'yan adawa wajen tsayar da mutum guda a matsayin dan takara.

Sudan | Rikici | Wad Madani
Rikicin Sudan ya ta'azzara, inda ya kai babban birnin mafaka na Wad MadaniHoto: AFP

"Sabuwar nasara ga mayakan Sudan. Garin Wad Madani da ke kan Kogin Nilu ya fada hannun mayakan tawayen RSF". Wannan shi ne taken labarin da jaridar die Tageszeitung ta wallafa kan halin da ake ciki game da yakin Sudan da ya haifar da karuwar dubban 'yan gudun hijira. Jaridar ta ce shekaru biyar bayan fara zanga-zangar lumana ta adawa da mulkin kama-karya a Sudan wanda ya rikide zuwa boren al'ummar kasar da ma juyin mulkin soja a shekara ta 2019, yakin da ake yi tsakanin manyan hafsoshin sojojin kasar biyu a yanzu ya kai wani sabon mataki. Garin Wad Madani mai tazarar kilomita 200 da Kudu maso Gabashin Khartoum babban birnin kasar, ya fada hannun mayakan sa-kai na RSF.

Karin Bayani: Jaridun Jamus sun sake duba rikice-rikice a Afirka

A safiyar Litinin ne dai kwamandan sojojin yankin ya mika birnin mai mutane dubu 700 bayan shafe kwanaki uku ana gwabza kazamin fada a kananan garuruwan da ke wajen birnin kafin a kai Wad Madani din, kamar yadda kafafen yada labaran Sudan suka ruwaito. Tuni dai bangarorin biyu suka tabbatar da hakan. Kame Wad Madani ne babbar nasarar da RSF ta samu, tun bayan da ta mamaye mafi yawan manyan garuruwan yankin Darfur na yammacin Sudan a watan Oktobar bana.
Ita kuwa jaridar Zeit Online ta yi sharhi ne game da ziyarar da ministar harkokin wajen Jamus ta kai birnin Kigalin, inda ta yaba da gina kamfanin sarrafa allurar riga-kafi na farko Ruwanda. Annalena Baerbock ta yi alkawarin goyon bayan Jamus da Tarayyar Turai ga kasashen Afirka, wajen yaki da da annoba da sauran cututtuka. Ziyarar ta Baerbock na bangaren halartar wani taron da aka yi ne a Kigali babban birnin Ruwandan, inda kamfanin harhada magungunan na Mainz Biontech ya gabatar da wata cibiya ta samar da alluran riga-kafi na mRNA ta farko a nahiyar Afirka.

Ruwanda | Kigali | Annalena Baerbock | Ziyara | Alaka
Ministan harkokin wajen Ruwanda Vincent Biruta da ta Jamus Annalena Baerbock Hoto: Florian Gaertner/photothek/picture alliance