1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shekaru bakwai ba labarin sauran 'yan matan Chibok

April 14, 2021

Shekaru bakwai bayan satar 'yan mata 'yan makaranta na Chibok kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakin dan adama ta ce babu wani darasi da Najeriya ta dauka daga satar da ke zama na farko a kasar.

https://p.dw.com/p/3s1od
Nigeria Region Borno Boko Haram
Hoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

An dai share shekaru har bakwai ana ta hawaye, sai dai kuma har ya zuwa yanzu babu alamun 'yan mata sama da dari da 'yan kungiya ta Boko Haram suka sace. To sai dai kuma kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakkin bil'ada tace mahukuntan Najeriya ba su dauki darasi daga satar da ta bude babin kwasar 'yan makarantan a cikin neman fansa ba.

Karin Bayani:Kungiyar fafutuka ta BBOG ta yi jerin gwano a Abuja

Amnesty dai ta ce har yanzu babu wani hukunci kan barayin yaran na Chibok dama ragowar yan uwansu da suka shiga hannu a sassa daban daban cikin arewacin tarrayar Najeriya.

Nigeria | Mutter mit Fotos ihrer 2014 entführten Tochter
Hoto: Thomson Reuters Foundation/O. Okakpu

Kimanin yara 640 'yan makaranta ne dai kungiyar ta ce an sace a tsakanin shekarar da ta shude zuwa bana a wani abin da ke zaman sabuwar al'adar da ta samo asali daga Chibok. Dubban yara ne dai a fada ta kungiyar suka yi asarar dama ta karatu sakamakon rufe makarantu fiye da 600 a sassa daban-daban na arewacin Najeriya inda al'adar satar 'yan makaranta ta yi aure take shirin tarewa.

Karin Bayani:Najeriya: 'Yan matan Chibok 100 sun rasu

Kungiyar da cibiyarta ke birnin london dai ta zargi Gwamnatin tarrayar Najeriya da gazawa wajen kare hakkin yara na kasar, a cikin yanayin da karatu na zamani ke neman komawa batu na mutuwa ko kuma yin rai. Auwal Musa Rafsanjani na zaman shugaban kungiyar a Najeriya, da kuma ya ce cin zarafin yaran ya kai ga ko'ina bayan 'yan makarantar.