1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Azumin watan Ramadana a sassan duniya daban-daban

July 18, 2013

A duk shekara daidai wannan lokaci al'ummar Musulmi a duniya baki daya suna azumin watan Ramadana daya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar.

https://p.dw.com/p/19AGk
Ramadan in Bagdad - Irak Beschreibung: Ramadan in verschiedenen Orten der irakischen Hauptstadt Bagdad. Copyright: DW/Munaf Al-Saidy Alle Bilder sind von DW Korrespondent in Bagdad (Munaf al-saidy), wurden in 2013 aufgenommen, wurden im Irak aufgenommen, sind von DW honoriert. Der Korrespondent (Munaf al-saidy) hat uns versichert, dass alle Bilder von ihm stammen. Der Korrespondent (Munaf al-saidy) übernimmt daher die Verantwortung für alle Bilder. Der Korrespondent (Munaf al-saidy) hat die Bilder mit verschiedenen Kameras aufgenommen. Alle Bilder stehen zeitliche unbeschränkt für DW zu verfügen, und alle Bilder sind für eine Bildergalerie für Morgen 12.07.2013 bestellt. Zulieferer: Zemen Al-Bedry
Hoto: DW/Munaf Al-Saidy

Musulmai a nan tarayyar Jamus sun bi sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen gudanar da wannan aiki na ibada. Sai dai a bana kasancewa watan na Ramadana ya zo ne a lokacin bazara a kasashen Turai da kuma arewacin Amirka inda tsawon rana kan kai kimanin awowi 19 ga kuma tsananin zafi, ya sa wasu Musulman dake aikin karfi, sun ajiye azumin har sai lokacin da yanayi ya canja.