1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barin wuta a kan Boko Haram

Lateefa Mustapha Ja'afarDecember 29, 2014

Gwamnatin kasar Kamaru ta ce ta kaddamar da kai hare-hare ta sama a kan kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1EC9H
Hoto: Getty Images/Afp/Reinnier Kaze

Wata sanarawa da gwamnatin Kamarun ta fitar, ta nunar da cewa sojojin kasar sun jefa bama-bamai guda biyu da kuma yin barin wuta a kan 'yan kungiyar ta Boko Haram su 1,000 da suka mamaye sansanin sojoji na Achigachia wanda kuma hakan ya tilastawa 'yan ta'addan tserewa. Sanarwar ta kara da cewa mayakan na Boko Haram sun kai hari a wasu kauyuka biyar da ke arewaci a kan iyakar kasar da Najeriya kafin daga bisani su mamaye sansanin sojojin. Shugaba Paul Biya na Kamaru ne dai ya ba da umurnin kai hare-hare ta sama a kan 'yan Boko Haram din biyo bayan sauya salon hare-haren su da suka yi. Rikicin na Boko Haram dai da ya addabi Najeriya kusan shekaru biyar ke nan, ya hallaka rayuka da dama tare da tilastawa al'ummar yankunan da rikicin ya fi kamari tserewa zuwa kasashe makwabta irin su Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar.