1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka na fama da karancin riga-kafi

February 4, 2021

A nahiyar Turai, aikin yi wa mutane allurar riga-kafin corona yana tafiyar hawainiya, yayin da a nahiyar Afirka a wurare da dama ba a ko fara allurar ba.

https://p.dw.com/p/3otTR
Weltspiegel 02.02.2021 | Serbien Belgrad | Impfstoff aus Russland & China
Tallafin allurorin riga-kafin corona daga Chaina da Rasha zuwa AfirkaHoto: Oliver Bunic/AFP/Getty Images

Kasar Chaina na son ta yi amfani da wannan dama ba kawai saboda taimakon jin kai ba, watakila saboda kasuwanci da samun karin angizo a Afirka. Yanzu a fadin duniya an fi bukatar alluran riga-kafin cutar corona. Sai dai na kamfanonin Pfizer da Biontech da Moderna da AstraZeneca sun yi karanci, saboda haka sai kasashe masu arziki ne ke iya samunsu. Kungiyar People's Vaccine Alliance ta ruwaito cewa kasashe masu arziki da ke da kaso 14 cikin 100 na yawan al'ummar duniya, sun saye fiye da rabin alluran masu inganci.

Karin Bayani:An dage shirin riga-kafin COVID-19 a Najeriya

Afirka kuwa na sahun karshe, kuma kungiyar Economist Intelligence Unit ta ce da yawa daga cikin kasashen Afirka, ba za su samu alluran ba har sai watan Afrilun shekarar 2022. Kawo yanzu dai Afirka ta yi odar miliyan 900 na allurar.

Cibiyar binciken cututtuka masu yaduwa a Afirka ta ce, nahiyar za ta bukaci kimanin miliyan daya da dubu 500 na riga-kafin coronan, domin yi wa kaso 60 cikin 100 na al'umarta allurar riga-kafin da kudinsu gaba daya zai kai dalar Amirka miliyan dubu 10. Wannan abin damuwa ne kamar yadda ministan kiwon lafiya na kasar Kenya Mutahi Kagwe ya shaidawa DW.

Karin Bayani: Rudani kan shirin samar da riga-kafin corona a Najeriya

Tuni dai Afirka ta Kudu ta samu miliyan daya na allurar riga-kafin kamfanin AstraZeneca daga Indiya. Ruwanda ta yi odar miliyan daya daga kamfanin Pfizer da Moderna na alluran na COVID-19 da ake sa rai za a kai mata a cikin watan nan na Fabrairu. Yuganda kuma na sa ran samun nata alluran daga kamfanonin Moderna da Pfizer da AstraZeneca a cikin watan Afrilu. Hukumar Lafiyar ta Duniya wato WHO, da wani kawance da ake kira GAVI sun dukufa wajen ganin an yi adalci a rabon alluran riga-kafin a kasashe matalauta karkashin wani shiri mai suna COVAX da ke fatan kai allurai miliyan dubu daya da dubu 300 zuwa kasashe masu karamin karfi 92 a karshen shekara. Sai dai alluran da Hukumar WHO ta aminta da su ne kadai, wato kamar na kamfanin Pfizer ke cikin wannan shiri.
Wata matsalar kumma ita ce riga-kafin  kamfanonin magungunan na kasashen yamma, ba a yi su saboda yankuna masu zafi ba. Saboda haka wasu kasashen Afirka ke neman alluran riga-kafin daga Chaina, kamar na kamfanin Sinopharm, inji Eric Olander na wani shirin aiki tare tsakanin Chaina da Afirka.

Japan | Sagamihara | Brandneue Gefriergeräte sind in einem Lagerhaus bei Kanou Reiki zu sehen
Alluran rigakafin na bukatar yanayin sanyiHoto: Eugene Hoshiko/AP Photo/picture alliance

Karin Bayani: Cin zarafin 'yan Afirka a Chaina kan COVID-19

A nasu bangaren Chaina da Rasha na jaddada cewa,za a iya adana alluran riga-kafinsu cikin sauki ba dole ne su kasance a daskare ba. Tun a cikin watan Mayun 2020 shugaban Chaina Xi Jinping ya ce, an bayar da muhimmanci ga yanayin kasashen Afirka wajen samar da alluran riga-kafin na kasarsa. Ko da yake kungiyar EU ta ba wa WHO kudi masu yawa domin samar da alluran ga Afirka, amma tuni Chaina ta shirya tsab wajen raba magungunan. Wato kenan Chaina ka iya samun karin angizo a nahiyar ta Afirka.