1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Danbarwar siyasar Adamawan Najeriya

Ubale MusaOctober 9, 2014

Kasa da sa'oi 24 da hukuncin da ya kai ga sauyi na bazata a jihar Adamawa a Tarayyar Najeriya, masu ruwa da tsaki a batun siyasar kasar na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan hukuncin.

https://p.dw.com/p/1DSng
Hoto: DW/K. Gänsler

Sauyin da aka samu dai ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotu a babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja ya kai ga karshen fatan zakaran gwajin dafi na zabuka a shekarar dake tafe a tudu da gangaren kasar dake fuskantar rikici na tsaro. Tuni ma dai har ita kanta hukumar zaben kasar ta INEC ta ce ta shirya tsaf da nufin gwada sa'arta da ma watakila ba marada kunya a kokarin kaiwa ga zaben na jihar da ya dauki hankali dama haifar da damuwa ta makomar kasar ta Najeriya a shekarar dake tafe, kafin daga baya wata kotu a Abuja ta yanke kauna kan kowa tare da umartar sake mayar da tsohon tsari cikin jihar da daukacin jam'iyyun ke matukar burin tabbatar da samun nasara a ciki.

Hukuncin kuma da ya jawo muhawara cikin kasar kama daga su kansu masu ruwa da tsaki da siyasar Adamawa da ma masu kallon ta a nesa kuma ke mata fata na alamu na juma'arsu kyakkyawa a siyasa.

Wahlen Nigeria Wahlausgang
Wasu matasa a lokutan zabe a NajeriyaHoto: AP

Bayyana mabanbantan ra'ayoyi

Duk da cewar dai lale da maharbin na zaman karatun jam'iyyun kasar, fassarar ma'anar sabon tsarin na jihar Adamawa dai na banbanta daga fage zuwa fage na siyasar kasar. Injiniya Buba Galadima dai na zaman jigo a cikin jam'iyyar APC ta adawa kuma a fadarsa hukuncin kotun na zaman ta leko sannan ta sake komawa ga jam'iyyarsu da tai shirin kwatar Adamawar ko ta halin kaka yana mai cewa ...

"Dama take taken PDP ya nuna cewar sun tsorata sai suka nemi amfani da 'yan sanda da soja sun manta cewar al'ummar arewa maso gabas sun daina tsoron soja, wannan tsoro ne ya sa suka matsawa kotu ta ajiye shari'ar tabbatar da hukuncin halascin Nyako da aka tsara yankewa zuwa 16 ga wata suka dauko wannan shari'a dake kwance ta Bala Ngilari."

Akwai aiki ja a gaban sabon gwamnan

To sai dai kuma in ta saba na zaman karatun APC, ga 'yar uwarta PDP dai wai rushen zaben na zaman kokari na ceto jam'iyyar daga jin kunya a zaben da aka kai ga samar da dan takarar mara inganci amma kuma ke da jan aikin hada kan makiya ta bangare daban-daban a cewar Dr. Umar Ardo da ya nemi tsayawa PDP takara a rusasshen zaben.

Murtala Nyako
Tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala NyakoHoto: DW/U. Shehu

"Shari'ar kotun nan ta fidda PDP daga kunya ta fitar da ita cikin rigima ta fitar da ita daga rashin tabbas ta bata tabbas. Babbar damuwar gwamna ita ce shi ya ci amanar gwamnansa Nyako da mukarrabansa da suka tafi APC ya dawo yace baya yi ya dawo PDP, sannan sai PDP taci amanarsa ta tsaya aka kore shi, sannan ta baiwa wanda ya kore shi takara. Saboda haka yanzu yadda zai hada wanda yaci amana da wadanda suka ci amanarsa su hadu su kafa gwamnati shine a gabansa."

Abun jira a gani dai na zaman sauke karatun na cin amana a tsakanin juna cikin jihar da ake yi wa kallon ta gaba-gaba ga batun na siyasa a arewacin kasar da ma Tarayyar Najeriya ga James Bala Ngilarin da har yanzu yake tsallen murnar karensa ya kama zaki.