1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar zabe cikin annobar corona

Salissou Boukari AH
January 15, 2021

A Jamhuriyar Nijar manyan zabukan kasar da suka gudana sun kasan ce ne a cikin babban kalubale na barazanar kamuwa da cutar nan ta Coronavirus wadda a halin yanzu ake samun mutane da dama da ke kamuwa da ita.

https://p.dw.com/p/3nyhZ
Niger Tillabéri | Wahlen
Hoto: Marou I. Madougou/DW

Hukumar zabe dai mai zaman kanta tare da hadin gwiwar likitoci ta dauki matakai musamman ma dangane da halin da ake ciki na cutar Coronavirus mai saurin yaduwa a tsakanin al’umma, inda a wurare da dama hukumar ta dauki matakan da idan an yi amfani da su za a kai ga samun kariya. Da yake magana kan wannan batu mai magana da yawun hukumar zaben kasar ta Nijar CENI Malam Wada Nafiou, bayan ya isar da godiyar hukumar zaben ga yan Nijar da suka fito dafifi suka yi zabe, da kuma wadanda suka kama zabukan suka gudana, ya yi kira ga jama’a da su kiyaye matakan kariya na corona a lokacin zabe. Wannan batu na zabe da corona shi ne shirin Darasin rayuwa ya duba idan ana son karin bayyani daga kasa za a iya sauraron sauti.