1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar haramta sanya hijabi a Diffa

Larwana Mala Hami/USUJuly 28, 2015

A yayinda Boko Haram ke kara zafafa hare-hare ta hanyar yin kunar bakin wake a kasashen da ke makobtaka da tafkin Chadi gwamnatin Nijar ta kafa dokar haramta wa mata sa hijabi a fadin yankin Diffa.

https://p.dw.com/p/1G6V4
Niger Frauen vor Wahllokal in Tahoua
Hoto: DW

Bayan da hukumomi a Jamhuriyar Kamaru da Chadi da ke cikin hadakar rundunar kawance mai yaki da Boko Haram, sun kafa dokar haramta sa hijabi a kokarin su na magance hare-haren kunar bakin wake da 'yan kungiyar Boko Haram suke aikatawa a baya-bayan nan, inda hakan ke ci gaba da hallaka rayukan al'umma. Hakan ya tilastawa gwamnatin jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar ta bi sahu a farkon wanan mako ta hanyar kafa makamanciyar wanan doka ta haramta sa hijabi. Malam Salisu Garba shi ne shugaban majalisar malaman kungiyar Ahali Sunna yankin Diffa, karin bayani ya yi game da yadda suka dauki dokar.

Bayan mazauna babban birnin kusan a ce dari bisa dari sun yi marhabin da dokar, to ko wane tasiri dokar ke iya yi a fannin tsaro ga, Maman Dan Buzuwa wani tsohon soja mai ritaya da ke sharhi ba kan lamarin tsaro daga Damagaram, kuma acewarsa matakin yana da mahimmanci ta fannin tsaro.

To sai dai har kawo lokacin hada wanan rohoto daga bangaren hukuma, musaman gwamnatin jihar ta Diffa, ba wanda ya dauki wayar DW domin karin haske. Inda hatta da sakon waya da aka aike ba a samu amsa ba.

Wata 'yar Nijar daure da gyale
Hoto: DW/T. Amadou