1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar takaita gudun hijira a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou/PAWMay 12, 2015

Majalisar dokokin Nijar, ta amince da wata dokar dake hana yawan shige da ficen 'yan ci-rani da bakin haure zuwa wasu kasashe ba tare da ka’ida ba.

https://p.dw.com/p/1FOia
Afrika überladener LKW in der Sahara
Hoto: imago/alimdi

Dokar za ta shafi masu kulawa da sufurin jama'ar da ma su kansu masu anniyar zuwa ci-rani, da wadanda ke shigowa ta kasar Nijar domin tsallakwa. Wannan matakin na majalisar da ta dauka a jiya na zuwa ne a yayin da batun zuwa cin rani daga ciki da wajen Nijar din ke addabar mutane.

Da maraicen litini (11.05.2015) ne dai majalisar dokokin kasar ta Nijar ta rattaba hannu a kan dokar da kuri'a 82 daga cikin yan majalisun dokokin 113 da zummar rage kaifin yawan bakin haure da tsallakawar yan ci-rani na cikin gida da waje domin zuwa kasashen na Afrika ta arewa da zummar yin bida ko bara ga wasusun, a yayinda wasun kuwa manufofinsu shi ne na zuwa kasashen turai, dokar dai ta tanadi matakan hukunta wadanda aka kama da laifin yin safarar ko hada baki don cin nasara ga tafiyar da bata da tabbas.

Flucht über den Tschadsee
'Yan gudun hijirar sun mayar da Nijar tamkar mashiga ta zuwa TuraiHoto: picture-alliance/dpa/Palitza

Dalilin sanya wannan doka

Wannan dokar dai na zuwa ne a yayinda kasar ta jima tana jimamin ‘ya ‘yanta da dama da suka halaka a hamadar sahara sakamakon zuwa cin rani a ketare, ko ba'idinsa ma wasu 'yan kasashen Afirka na mayar da Nijar tamkar wata mashiga domin tsallakawa zuwa Afirka ta arewa daga nan su wuce zuwa turai, Honorable Shafi'u Magarya na daya daga cikin yan majalisun dokokin da suka jefa kuri'a akan wannan dokar

"Duk yawanci yan Afrika masu ketawa su je turai ta barauniyar hanya ta Nijar suke biyowa to wannan abin ya sa muka saka doka kuma wannan abu ne ba mai kyau ba kuma jirgin ruwan da ake dorawa mutun hamsin sai kaga an dora mai dari da hamsi duk wanda zai shigo nijer ba wai an hana mutun ya shigo ne ba a'a to ya shigo da takarda a san ko waye daga ina yake hakan kuma idan ma nijer din ya fita can inda zai je a san da daga nijer ya biyo ga kuma inda zashi saboda yana da takardu."

Flucht über den Tschadsee
Kwale-kwalen da ake daukarsu ba su da karkoHoto: picture-alliance/dpa/Palitza

Wasu yarjeniyoyi na kawo tsaiko wajen bincike
Ko baya ga makwabtaka da kasashen yammaci da na arewacin Afrika jamhuriyar Nijar na da dimbin yarjejeniyoyi, da ke hana hukumomin tsaronta yin binciken kwakwab na takardun baki daga Afirka ta yamma wanda wani bin daga yankin ne bakin hauren ke tsallakawa, abubuwan da suka saka masana da dama yin bitar irin tasirin da dokar za ta iya yi wacce 'yan majalisun dokokin kasar suka sakawa hannu to amma sai dai a cewar Honorable Saidu Amma Na jam'iyyar CDS Rahma dokar ba shakka zata iya yin tasiri

"Ai babu abinda zai yi maganin wannan abin idan ba doka ba kuma zata yi tasiri idan har ya kasance wadanda aka sa aikin sun yi aikinsu to yaya za'a iya cewar dokar zata hana mutane zuwako fita? ya ce a'a ba zata iya hana mutane fita ba amma zata rage masifar yawan fitar da mutane ke yi da yawan hallaka mutane"

Dokar dai yanzu hakan tana a gaban gwamnati domin rattaba mata hannu tare da hakikanceta a matsayin dokar da ke shirin yin bulala ga duk wanda ya takata ko aka kama da laifi.