1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sabbin hare hare a Dosso

Salissou Boukari
February 14, 2019

Sannu a hankali lamarin tsaro na zama wani babban kalubale a wasu yankuna da dama na Jamhuriyar Nijar. Na baya bayan nan shi ne harin da aka kai wa wasu jandarmomi a garin Bagaji da ke cikin jihar Dosso

https://p.dw.com/p/3DNfT
Niger Paramilitäreinheit der Polizei bei Übung
Hoto: picture-alliance/AP Photo/C. Petesch

Yayın da ake cikin cece-kuce ne dai na saka dokar takaita zirga zirgar jama'a da ta ababen hawa a cikin birnin Tillabery, da ke yankin yammacin Nijar nan sakamakon barazanar masu kai hare-hare, sai kuma aka ji wannan sabon hari na garin Bagaji wanda ya rutsa da wasu jami'an tsaro na jandarmomi uku da kuma wani farar hulla guda.

Daga nasu bangare ‘yan majalisar dokoki na kasa wanda sune wakillan al'umma na jihohin Dosso da ma Tillabery, na biyar wannan lamari sau da kafa, kuma a cewar Korone Masani, dan majalisar dokoki na kasa da ya fito daga yankin da harin ya afku, bayan ya yi Allah wadai da kisan jandarmomin ya kuma nuna fargabarsa kan makomar tsaro da tattalin arzikin yankin.

Bayan wannan matsala ta harin garin Bagaji, saka dokar ta-baci har a birnin Tillabery ya haifar da cece-kuce, inda al'ummar yankin suka kira yajin aikin kauracewa saye da sayarwa don nuna bakin cikinsu.

A halin yanzu dai mahakumata da ma wakillan al'umma sun dukufa ga yin kira zuwa ga al'umma a ko'ina cikin fadin kasar ta Nijar da su kasance masu buda idanunsu domin gane muyagun mutane da ke shigowa da nufin cutar da alluma ko kuma mayar da hannun agogo baya ga kokarin da ake na samun tabbatacen zaman lafiya.