1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da zabiya ke ciki a Jamhuriyar Nijar

March 6, 2014

Kungiyar zabiya ta Jamhuriyar Nijar mai suna ANAN ta koka dangane da abin da ta kira kyama da wariya da mutane ke nuna wa 'ya'yanta.

https://p.dw.com/p/1BLJD
Hoto: Carlos Litulo

Kungiyar zabiyan ta yi kira ga gwamnatin Nijar da ma duk masu hannu da shuni a ciki da ma wajen kasar da su taimaka mata wajen samar da matakan inganta halin rayuwar mambobinta da ke kasar. Talauci da rashin aikin yi da bala'in yanayin zafin rana da ake fuskanta a wannan yanki na Sahara, a mafi yawancin lokuta na shekara na jawo musu illoli a rayuwarsu.

Sai dai kawo yanzu babu wasu ingantattun alkaluma dangane da adadin yawan zabiya da ke a kasar ta Nijar. Amma ko da ya ke, ba sa furskantar matsalolin kisan gilla kamar yadda takwarorinsu na wasu kasashen Afirka su ke fuskanta, a inda ake yin tsafe-tsafe da sasan jikin nasu, amma zabiya a kasar Niger na fama da irin nasu matsaloli na rayuwa daban- daban, kamar dai yanda Malama Zeinabu Seidu Sakatariyar kungiyar zabayan ta kasar Nijar ta ke mani bayani.

Jake Epelle
Zabiyan Afirka na fadakarwa kan halin rayuwarsuHoto: DW/N. Aghaji

"Idan mun fita waje sai mutane su yi ta tsokalar mu, suna mana wasu abubuwa tamkar dai mu ba mutane ne ba, shi ya sa wasu ko ka tafi gidajan su basa fitowa sai su shige kuryar daki."

Su ma dai daga nasu bangare iyayen wadannan bayin Allah, wanda akasarin su ba zabiya ba ne, na fama su ma da nasu matsalolin na yau da kullum. Malama Aissatou Amadou ta na da 'y'aya hudu, amma kuma biyu daga cikin su zabaya ne. Ta bayyana yadda halin rayuwar tasu ta ke ita da 'y'ayan nata ta na mai cewa.

"Yaran suna da matsaloli musamman ma idan akwai rana to zafin ranar nan na bata musu jiki, domin bana mantawa wata shekara da akayi rana sosai, yaro na mai sunan Sherif saida fatar jikin sa ta fara tashi sabili da zafi, abun akwai ban tausayi domin a lokacin nan shi kadai ne Zabiya yayi ta kuka ."

A halin yanzu dai, an samu kimanin watanni hudu da zabiyan kasar ta Nijar su ka girka tasu kungiya, a wani mataki na neman kare hakkokinsu, da ma neman inganta rayuwarsu a wannan kasa. Sai dai har kawo yanzu ba su da wata cibiya tasu ta kansu sannan a yanzu haka, daga cikin zabiya 28 da su ka kafa wanann kungiya ba wani mai aikin yi. Akan haka Sakatariyar wannan kungiya ta Zabiyan kasar ta Nijar, Aissatou Amadou, ta yi shelar neman agaji ta na mai cewa.

Rene und Clifford Bouma aus Kamerun
Zabiyan kasashen Afirka na hada karfi da karfeHoto: Rene und Clifford Bouma

"Taimako dai muke bukata daga gwamnati, ko daga duk wani mai halin da kan iya taimaka mana, domin matsalar rana na bamu wahala sai a samu matsalar gani da idanu, domin da dama na barin makaranta ne sabili da matsalar idanu dan haka muna bukatar taimako."

Mawallafi: Gazali Abdou Tassaoua
Edita : Salissou Boukari/ Mouhamadou Awal Balarabe