1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe yara guda bakwai a Maradi

Abdourahamane Hassane MAB
February 20, 2022

An kashe yara guda bakwai kana wasu biyar suka jikkata a wani harin kuskure ta jiragen sama na yaki da rundunar sojojin Najeriya ta kai a kan iyaka da Nijar a Jihar Maradi.

https://p.dw.com/p/47JKY
Nigerianischer Soldat
Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP

Gwamna Jihar Maradi Chaibu Abubakar ya ce harin wanda dakarun Najeriya suka kai bisa kuskure kan zaton cewar 'yan fashin daji ne, ya faru a garin Nachade da ke a yankin Madarounfa da ke kan iyaka da Najeriya. Yankunan da dama da ke cikin Jihar Maradi wadanda ke kan iyaka da Najeriya na fuskantar hare-hare na 'yan fashin dajin.