1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar zaben Nijar ta yi sabon shugaba

Mahaman Kanta daga YamaiApril 30, 2015

Alkali Ibrahima Goube da Lawya Kader Oumarou sanda sun zama shugaba da mataimakin shugaban hukumar zaben jamhuriyar Nijar bayan da CNDP ta yi mahawara

https://p.dw.com/p/1FIPY
Hoto: DW/M. Kanta
So biyu majalisar sulhu tsakanin 'yan siyasa ta yi zama don samar da sabon shugaban hukumar zabe a Nijar ba tare da hakarta ta cimma ruwa ba. Amma kuma a wannan karon an samun daidaito tsakanin bangaren da ke mulki da kuma 'yan adawa, inda aka zabi alkali Ibrahima Goube a matsayin shugaban CENI yayin da lawya Kader Oumarou Sanda ya zama mataimakin shugaban wannan hukumar.
Sai dai duk da cewa sun amince da wannan nadi, amma kuma 'yan adawan Nijar suka ce ba dole ba ne a nada alkali ba kamar yadda bangaren gwamnati ta yi ikirari.
Kungiyar alkalai ta SAMAN ce ta mika sunan Ibrahima Goube don nadashi a matsayin shugaban CENI. Yayin da shugaban kasa ya mika sunayen mutane uku da suka cancata a nada a mukamin mataimaki, inda aka zabi daya daga cikinsu.
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
'Ya adawan Nijar sun zargi shugaba Issoufou da yin katsaladanHoto: F. Batiche/AFP/Getty Images
Kungiyoyi matan Jamhuriyar Nijar ne ya kamata su mika sunan wadanda za a nada a matsayin mataimakin CENI na biyu. Yayin da su ma kungiyoyin farar hula suke da nasu kason. Sai idan shugaba Issoufou ya sa hannu kan takadar nadasu sannan sun yi rantsuwa da alkura'ani ne shugabbnnin hukumar zaben Nijar za su fara aiki.
Zaben 'yan majalisa na farkon shekara mai zuwa ne zai zame wa sabbin shugabannin CENI zakaran gwajin dafi. Yayin da zaben shugaban kasa kuma zai gudana daga bisani.