1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Nijar sun tsare Nouhou Arzika

Usman ShehuJuly 18, 2014

An dai tsare fitaccen dan kungiyar farar hulan ne bayan da ya furta wasu kalamai da suka shafi ziyarar shugaban kasar Faransa Francois Hollande a yau Jumma'a a Nijar.

https://p.dw.com/p/1Ceqn
Niger Mahamadou Issoufou
Hoto: picture-alliance/dpa

Da asubahin wannan Jumma'ar ne 'yan sanda suka cafke Nouhou Arzika da Ali Idrissa shugabannin kawance kungiyoyin "Sauvons Le Niger". Kawo yanzu dai babu wani bayani a game da dalillan kamasu. Amma waklinmu a Yamai Gazali Abdou Tasawa ya ce matakin ba zai rasa nasaba da sanarwar da suka fitar a ranar Alhais ba, dangane da zuwan shugaban kasar Faransa Francois Holland a NIjar.

Shugabannin kungiyoyin dai sun soki lamirin kasar ta Faransa a kan abun da su ka kira, zalumcin da ta ke yi wa Nijar. Kana sun bukaci jama'a da su fito da kellaye masu launin masara, domin nuna wa shugaban kasar ta Faransa adawarsu.

A wannan Jumma'ar ce shugaban kasar ta Faransa Francois Hollande ke isa Jamhuriyar ta Nijar domin gudanar da wata ziyar aiki, a rangadin wasu kasashen Afirka renon Faransa da ya ke yi, wadanda suka hada da Chadi da kuma Côte d' Ivoire.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe