1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta dokokin sadarwa a ECOWAS

Abdoulaye Mamane Amadou
May 4, 2017

'Yan majalisun dokokin kasahen kungiyar ECOWAS ko CEDEAO sun gudanar da mahawara a Nijar kan yadda za a ci moriyar kafafen sadarwa na zamani, da kuma samar da muhimman dokokin kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/2cOrs
Äthiopien Addis Abeba Universität Kommunikation Internetsperre
Amfani da hanyoyin sadarwa ya zama jiki tsakanin al'ummaHoto: DW/J. Jeffrey

Babban makasudin taron na birnin Yamai da 'yan majalisun dokokin kungiyar ta CEDEAO ko kuma ECOWAS ke halarta, shi ne na cimma matsaya daya wajen samar da dubaru da fasahohi irin na siyasa, da nufin bunkasa fannonin sadarwa irin na zamani tare da kuma da wayar da kan 'yan majalisun kasashen kan irin alfanun da ke tattare da tsarin, domin cimma burin kungiyar ta hanyar shigar da dokoki da wasu ka'idojin da ka iya kasancewa na bai daya da zummar bada kariya ga jama'a, dama taka birki ga tarin matsalolin da ake samu a fannonin. Honorable Korone Massani Dan majalisar dokoki na Jamhuriyar Nijar kuma kwararre a fannin na sadarwa ya yi tsokaci:

Samar da fasahar sadarwa ta zamani a ko'ina
"Manufa ta farko ya kasance an dauki dokar a tsakanin kasashen ECOWAS ko CEDEO, kuma dokar ta amfani kasashen. Amma idan aka samar da doka, sai y kasance kasashe basu wuce uku ko hudu ne kawai ke amfani da ita ba, to ina amfanin ta? Abu na biyu kuwa shi ne ta yanda za a magance matsalolin da suka shafi Internet. Duba ka gani yanda matsalolin suka addabi wannan fasaha, amma kuma babu wata kasar da ke da wata doka da ake iya daukar hukunci ga wadanda suka aikata laifi a ciki, kuma akwai matsaloli da yawa."

Sai dai duk da matsalolin da a ke fuskanta da irin illolin da ke tattare da tsarin na fasahohin sadarwa na zamani, a share daya ana iya cewa an samu ci-gaba sosai da na'urori irin na zamani wanda taron na Yamai zai kara bada haske a kai don karfafa wa talakawa musamman mazauna karkara gwiwa, tare da fadakar da su yadda za su ci moriyar tsarin da ake ganin zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki. Honorable Mohamed Ogoshi Onawo shugaban rukunin 'yan majalisa ne masu lura da fannin na'urorin zamani a majalisar dokokin Tarayyar Najeriya:

Brasilien DW Akademie Workshop Rebecca MacKinnon
Fasahar zamani ta haynar sadarwaHoto: DW/S. Leidel

Amfani da hanyoyin sadarwa ya zama jiki
"Dole ne mu 'yan majalisa mu tashi don biyan bukatar talakawan da suka zabe mu ta ko wane fanni. Misali ni ina wakiltar kauyuka da dama da ke daukar dogon lokaci kafin su kai ga samun wutar lantarki. To dukaninsu mun kai cibiyoyin fasahar sadarwa, inda hakan ke taimaka musu kana ya taimaki dukkanin wadanda ba su da aikin yi da ma koyawa yara yadda ake zaman duniya."

Sai dai taron 'yan majalisun na zuwa ne a ya yin da al'ummomin kasashen ke fuskantar matsaloli na tsadar farashin sadarwa inda ake ci gaba da samun farashi mabambanta daga wata kasar zuwa wata, alhali kuwa kasashen sun rattaba hannu kan kasance wa a dunkule domin amfanin al'ummominsu. Dan majalisar dokoki Korone Massani ya ce yanzu haka kungiyar ta ECOWAS na kan hanyar kawo maslaha musamman ma a fannin sadarwa na wayar salula:
 

Afrika Facebook Nutzer Smartphone
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Samar da dokoki na bai daya zai taimaka

Symbolbild Afrika Medienentwicklung Digitale Medien
Matasa masu Amfani da shafuka na InternetHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

"Akwai dokokin da kungiyar ECOWAS ke shirin kawo wa kasahen don rattaba musu hannu wanda zai sa a samu rahusa kamar kana cikin kasar da ka ke idan ka buga tarho don ka biya a cikin farashi. A ce yanzu idan dan kasuwar Nijar ya je Kano sayayya dole ne sai ya sayi layin sadarwa na Kano, idan ba haka ba kudaden da zai kashe na sadarwa ga ko wane kira zai iya biyan fiye da jika ko 300 na Sefa."

An dai shafe tsawon yini biyu ana tafka muhawara tsakanin 'yan majalisun dokokin da masana da kwararru ta fannin sadarwa da hukumomin kasashen da kuma wakilan kungiyoyin fararen hula masu kare hakin masaya, don zama kunnuwa da idanun talakawan da ke amfani da fasahohin na zamani.