1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jama'a ta kwantar da hankalinta - Tanja Mahamadou

February 6, 2014

A karon farko tsohon shugaban jamhuriyar Nijar Tanja Mahamadou ya fito fili ya yi fira da manema labarai shekaru kusan hudu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi masa.

https://p.dw.com/p/1B3sH
Niger Tanja Mahamadou und Souley Oumarou
Hoto: DW/M. Kanta

Tsohon shugaban dai ya ambato batutuwa da dama ciki har da na kudaden da ya ce ya bari a baitulmalin gwamnatin, batun da a baya bayan nan gwamnatin kasar ta umarci kotu da ta saurari tsohon shugaban.

A cikin hirar da tsohon shugaban na Nijar ya yi da manema labara ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu a kan maganar kudaden da ake rudani kanta. Baya magana game da sauran abubuwa in ban a abu guda daya, wato sha'anin abinci ga 'yan Nijar da fatan Allah Ya raba su da masifar yunwa.

Samarwa da kasa da isasshen abinci

Niamey Niger Alltagsleben
Hoto: B.Hama/AFP/GettyImages

Tsohon shugaban dai ya ce a lokacin da ya kama mulki ba tarar da ko da buhu daya a rumbun hukumar OPVN ba. A saboda haka ya mayar da hankali wajen ganin kasar ta Nijar ta samu abinci a ko-ina ciki adin kasar. Kuma an samu sauyi mai ma'ana domin daga bisani rumbunan OPVN sun cika da abinci har ma babu wurin da za a ajiye wasu.

Ban da abincin akwai kuma ajiyar kudi ta OPVN miliyan dubu 11 wanda OPVN ke da damar amfani da su wajen sayen kayan abinci daga wurin talakawan kasa.

Na biyu a cewar tsohon shugaban shi ne da yake kusan miliyan dubu 100 za a bada lissafin inda suke, to sai a duba abubuwa na OPVN da abin da suka taimaka duka kamar kayakin noma kafin a yi jimillarsu sannan a tabbatar in maganar da yake ba haka ba ne.

Ministan kudi zai iya yin bayani

Tsohon shugaban na Nijar wanda aka fi sani da Baba Tanja ya yi kira da a gaiyaci ministan kudi ya ba da ba'asi a lokacin da aka yi wa gwamnatin tanja juyin mulki, nawa ne ska bari a batulmalin gwamnati. Domin shi kadai ne ya san wannan kuma shi kadai ne zai yin wannan magana, ba magana ce ta shugaban kasa ba.

Tanja Mahamadou
Hoto: DW/M. Kanta

Mahamadou Tanja ya ce babu ko da taro a gidansa ko a wata ajiyar banki dake waje, saboda haka jama'a ta kwantar a hankalinta. In ma da akwai wannan kudi a cikin ajiyar to ya ba wa 'yan kasa dama su je su dauka.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Pinado Abdu-Waba