1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan wanda zai gaji Paul Biya

March 24, 2021

A Kamaru, muhawara ta sake barkewa kan wanda ya kamata ya maye gurbin Shugaba Paul Biya mai shekaru 88 a duniya, a kan karagar mulki.

https://p.dw.com/p/3r3se
Kamerun Präsident Paul Biya
Shugaba Paul Biya na Kamaru Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Ana dai ambaton sunan Emmanuel Franck Biya babban dan Shugaba Paul Biya na Kamarun, a matsayin wanda yake iya maye gurbinsa. Hakan ya biyo bayan kira da wata jam'iyyar siyasa ke yi kan ya zama magajin mahaifinsa. Wani bidiyo da ya shafe mako guda ya na karade shafukan sada zumunta na zamani, na kira ga Frank Biya ya tsaya takara a zaben shekara ta 2025. Wannan kuwa na cikin farfaganda ko matsin lamba da wata kungiya da ta kunshi 'yan siyasa da 'yan kasuwa da wasu na kusa da bangaren mulki ke yi, domin ganin ya maye gurbin Paul Biya.

Karin Bayani: Karuwar take hakkin dan Adam a Kamaru

Duk da cewa wanda ake yunkurin domin sa bai bayyana matsayinsa ba har ya zuwa yanzu, amma wannan shi ne karo na biyu da wadanda suke dasawa da Frank Biya ke neman ya tsaya takara. Ko da yake hakarsu ba ta cimma ruwa ba a shekara ta 2013, amma jagoran wannan kungiyar da ake kira Frankist dan kasuwa Mohamed Rahim Noumeu ya ce Franck Biya zai kasance amintaccen shugaba ga kasar Kamaru. Tuni ma kungiyarsa ta kaddamar ta fara zawarcin 'yan Kamaru mazauna kasashen waje, domin neman hadin kansu.

Frankreich Proteste der Opposition Kameruns in Paris
'Yan Kamaru mazauna Turai, sun yi zanga-zangar adawa da shugabancin Paul BiyaHoto: AFP

Nathan Abomo shi ne jami'in yada labarai na kungiyar Mouvement citoyen des frankistes pour la paix et l'unité du Cameroun, ko kuma 'Franckist Citizen Movement for Peace and Unity in Kamaru: "Franck Emmanuel Olivier Biya ya bayyana a matsayin matashi da ya tattara duk wasu fasahohin da suka dace. Kasancewar ya rike mukamin mai ba da shawara na musamman ga Shugaba Paul Biya na kusan shekaru 25, a bayyane yake cewa yana da masaniya kan batutuwa masu mahimmanci a Kamaru, ya nakalci siyasar cikin gida da waje. Franck Biya mutum ne da ba ya nuna kai, dan kasuwa ne. Wannan na cikin dalilai da yawa da suka sanya muke kira gare shi."

Karin Bayani: Gwamnati na neman sulhu da 'yan awaren Kamaru

Wasu 'yan Kamaru sun fara nuna damuwa dangane da sake bijiro da batun Frank Biya a matsayin wanda ka iya gadon mahaifinsa, suna masu danganta wannan mataki da kama karya da salon mulki na gargajiya na da ya gaji ubansa, kamar yadda Faure Gnassingbé ya maye gurbin mahaifinsa a Togo yayin da  Ali Bongo ya gaji Omar Bongo a Gabon. Sai dai Olivier Bile malamin jami'a kuma shugaban jam'iyyar UFP, ya yi imanin cewa wannan yanayin da ba zai taba yiwuwa ba a Kamaru.

Bildkombo Emmanuel Franck Biya und Paul Biya
Emmanuel Franck Biya da mahaifinsa Shugaba Paul Biya na Kamaru

Tsarin mulki na kasar Kamaru ma ba ya bayar da damar da ya gaji ubansa a kan kujerar mulki. Sai dai kasar ta kasance a rukunin kasashen da suka kwaskware kundin tsarin mulkin domin bai wa Shugaba Paul Biya damar gudanar da salon mulkin mutu ka raba. Amma Patrice Siméon Mvomo mai sharhi kan al'amuran siyasa, ya ce tsarin mulkin Kamaru a bayyane yake: "Al'ummar Kamaru ne wadanda aka mika wa wuka da nama a kan batun  gadon mulki. Sashe na shida daga sakin layi na hudu ya fayyace cewa idan har shugaban kasar ya riga mu gidan gaskiya ko kuma ya kasa aiwatar da mulki, to shugaban rikon kwarya zai kasance shugaban majalisar dattawa. Shi ne ke da alhakin shirya zabuka akalla kwanaki 20 zuwa 40 bayan wannan cike gurbi. Dukkanin cibiyoyin an riga da an kafa su, don haka da su muke aiki. "

Yayin da ake jiran Franck Biya ya fayyace matsayinsa a kan mulkin Kamaru, ana yada jita-jita dangane da batun rikon kwarya nan gaba, saboda gazawar Shugaba Paul Biya na jagoranci kasar sakamakon tsufa da rashin lafiya.