1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Rashin filayen kiwo babbar matsala ga makiyaya

Issoufou Mamane AH
April 5, 2019

Kungiyoyin farar hula a Jamhuriyar Nijar na bayyana damuwarsu a game da yadda attajirai masu kudi ke sayen filayen da suke komawa mallakarsu abin da ke zaman cikas ga makiyaya a game da sha'ann kiwo.

https://p.dw.com/p/3GGYG
Nigeria Viehhirte
Hoto: picture-alliance/F. May

Daman dai matsalar canjin yanayi da kuma girma da garuruwa ke yi na sa da sannun a hankali ana rasa wasu filayen da makiyaya ke yin amfani da su don kiwo.To amma hali na baya-baya nan da ake fuskanta a Nijar na yadda masu kudi ke mallake filayen ta hanyar sayesu ya sa  al'amuran kiwon cikin wani mummunar hali.Tuni dai kungiyoyin farar hula suka nuna fargabansu a game da karancin filayen kiwon.