1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ceto wasu 'yan Nijar daga 'yan bindiga

January 19, 2021

Jami'an tsaro a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, sun kubutar da wasu mutane tara 'yan Jamhuriyar Nijar da 'yan bindiga suka sato daga garuruwansu suka kai su jihar ta Katsina sukai garkuwa da su.

https://p.dw.com/p/3o89g
Nigeria Katsina | Boko Haram-Angriff auf Schule | Freilassung
A kwanakin baya, jami'an tsaro sun ceto yara 'yan makaranta da aka sace a KatsinaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Za dai a iya cewa wanna ne karo na farko da mahukuntan jihar ta Katsina suka kubutar da wasu da aka yi garkuwa da su daga Jamhuriyar ta Nijar, kuma tuni gwamnan jihar ta Katsina Aminu Bello Masari ya bayar da umarnin mayar da su garuruwansu a jihar Maradi da ke Jamhuriyar ta Nijar, bayan da aka kai mutanen a fadar gwamnatin jihar bayan an kubutar da su.

Karin Bayani: Dakon mahukunta su ceto yaran da aka sace a Katsina

Sai dai gwamnan ya ce nasarar ci gaba da kubutar da mutanen da suke, ba sulhu ba ne saboda ba zai kara shiga yarjejeniyar sulhu da 'yan bindigar ba.
Masana tsaro a Najeriyar dai kamar Al-ameen Isa na da nasu hangen kan ceto 'yan Jamhuriyar ta Nijar da 'yan bindigar suka sato daga kasarsu tare da yin garkuwa da su.

Nigeria Katsina Sicherheit
Matasan jihar Katsina sun yi zanga-zanga kan matsalar tsaro Hoto: DW/H. Y. Jibiya

Karin Bayani: Najeriya: Ana zubar da jini a Arewa

Sannu a hankali dai mahukuntan jihar Katsina na ci gaba da karbo mutanan da 'yan bindigar suka sace domin neman kudin fansa ba tare da biyan ko sisi ba, a cewar mahukunta. Ko a makonni biyun da suka gabata ma, an yi nasarar ceto mutane 104 daga hannun maharan.