1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kawo karshen tsadar abinci a Najeriya

February 2, 2017

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa wanin kwamitin da zai duba dabarun magance matsalar tsadar abinci da al'ummar kasar ke kokawa a kansa a yanzu.

https://p.dw.com/p/2Wsl5
Nigeria Tomaten auf dem Markt in Port Harcourt
Hoto: DW/M. Bello

 A yunkurinta na rage radadin da ke kara tasiri tsakanin ma'aikata da talakawa a tarrayar Najeriya, gwamnatin kasar ta kama hanyar kawo karshen hauhawar farashi na abinci da ke barazana ga rayuwar 'yan kasar. A tsawon shekara guda dai farashin kayan abinci ya ninka da kusan kaso 200 zuwa 300 a kasar wadda yanzu ke fuskantar massasarar tattalin arziki. Ana dai ta'allaka sabon matsin da ya kai ga kara mayar da 'yan kasar 'yan rabbana ka wadata mu.

Duk da cewar dai kudi sun shiga hannun manoma kuma kasar na kara  kokari na habaka harkar noman zuwa sabuwar sana'a mafi farin jini, kara hauhawar farashin tsakanin ma'aikata da ke dogaro da albashi ya zuwa masu karamin karfi na birane dai na kara tayar da hankalin gwamnatin kasar da ke neman shawo kan matsalar tare da kafa wani kwamitin ministoci domin tunkarar lamari.

Afrika Soweto Stadtansichten Markt
Dubban 'yan Najeriya na kokawa kan matsin rayuwa sakamakon tsadar abinciHoto: picture-alliance/Dumont Bildarchiv/T. Schulze

Babban aikin kwaimitin mai ministoci bakwai dai  a fadar ministan yada labaran kasar Lai Muhammad na zaman bin diddigin asarar da kasar ke yi ga batun na abinci ko dai a gonaki ko kuma a kasuwanni na kasar. 

Gwamnati ta ce ta damu game da tashin farashi na kayan abinci da kuma cewar kayan abinci ba sa isa ga kasuwa in kuma har sun kai to kuma ba sa biyan bukatar 'yan kasar.

Babban aikin kwaimitin dai shi ne tabbatar da cewar an rage asarar da ake fuskanta ko dai a gonakin ko kuma a kasuwanni na kasar. Akwai kuma rahotannin saye kayan abincin tare da boye su a rumbuna da wasu attajirai ke yi domin neman riba. Sai dai koma ta ina gwamnatin kasar ke fatan farawa da nufin kaiwa ga shawo kan matsalar ta abinci dai, babbar mafita a fadar Isa Tafida Mafindi wanda babban manomi a  Abuja  shi ne saye amfani a hannu na manoma tare da sayar da shi a farashi mai tsada ga 'yan kasa.