1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta kama tsohon shugaban Jam'iyyar CPR mai adawa a Nijar

Gazali Abdu TasawaNovember 27, 2014

Shi dai Kasum Mokhtar matashi ne dan shekaru 36 da haihuwa da Allah ya yi wa daukaka a fagen siyasa. Ya rike mukamin ministan sadarwa kana kakakin gwamnati a lokacin gwamnatin Tanja Mamadu.

https://p.dw.com/p/1DvWE
Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

A bangare daya kuma wata kotun birnin Yamai ta tabbatar da matakin korar wasu shika-shikan Jami'yyar Lumana Afrika da uwar jam'iyyar ta kora a bisa zarginsu da karbar mukamai a cikin gwamnati ba tare da izinin uwar jam'iyyar tasu ba.

Binciken da wakilinmu a Yamai Gazali Abdou Tasawa ya gudanar, wata majiyar da ba ta so a bayyanata ba ta shaida cewa ana zargin Malam Kasum Mokhtar din da yin rub da ciki da dukiyar kasa da tara dukiya ta haram da yin cin hanci da rashawa da yin amfani da takardu na jabu da dai sauransu.

Hukumomin shari'ar dai sun aika aka zo da shi birnin Yamai inda aka gabatar da shi da farko a hukumar 'yan sanda ta Police Judiciare ta birnin, kafin daga bisani a gabatar da shi a gaban babban alkalin gwamnati wanda bayan ya saurare shi ya bada umarnin a fice da shi a gidan kurkukun garin Kollo da ke da nisa kilomita 25 da birnin Yamai, inda yanzu haka ake ci gaba da tsare shi.