1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Taro kan Sahel da Tafkin Chadi

Gazali Abdou Tasawa LMJ
March 24, 2021

An bude taron kasa da kasa kan batun inganta yanayin zamatankewar al'umma a kasashen yankin Sahel da na Tafkin Chadi, a Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/3r4Sv
Nigeria Tschadsee Konferenz
Shugabannin Afirka na taron neman mafita ga yankunan Tafkin Chadi da SahelHoto: State House, Abuja

Makasudin taron na yini biyu dai shi ne, hada kan masu ruwa da tsaki a cikin harkokin tsaro da na agaji wajen shawo kan matsalolin tsaro da na zamantakewa a kasashen na Sahel da na yankin Tafkin Chadi. Taron wanda ya samu halartar shugabannin sojoji da kwararru kan harkokin tsaro da kungiyoyin agaji, zai tattauna yadda kungiyoyin 'yan ta'adda suka yi kaka gida a wadannan yankuna biyu, inda suke aikata kisan ba gaira kan fararan hula da ma sojoji kamar yadda aka gani a makonni baya-bayan nan a jihohin Tillabery da Tahoua na Nijar da kuma a Mali.

Karin Bayani: Rundunar sojojin yankin tafkin Chadi ta gaza

Janar Abou Tarka shugaban hukumar koli mai kula da wanzar da zaman lafiya a Nijar, wacce ita ce ta shirya taron hadin gwiwa da hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya. Da yake jawabi a bikin bude wannan taro Maman Sadikou Sakataren zartarwa na kungiyar G5 Sahel, ya bayyana cewa daura da matakan soja da suke dauka kan 'yan ta'adda a yankin na Sahel, suna kuma samun nasara sakamkon tallafin kungiyoyin masu zaman kansu wajen sulhunta kabilun da ke rikici da una a wasu kasashen na Sahel da zummar inganta yanayin zamantakewa.

Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
'Yan ta'adda sun tilasta dubban mutane a yankunan Sahel da Tafkin Chadi gudun hijiraHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNDP ta bakin wakiliyarta a Nijar, ta jinjinawa Nijar din dangane da rawar da take takawa wajen rage kaifin matsalar tsaro da zamantakewa a yankin Difa na Yankin Tafkin Chadi da ta ce zai iya zama a bin misali: "Misalin da Nijar ta nuna wajen aiwatar da ayyukan inganta rayuwar al'umma a yankin Diffa, inda aka dama da mazauna yankin da kuma jagororinsu wajen aiwatar da duk tsarin da aka fito da shi. Abin jinjinawa ne, amma ya kamata a fadada shi zuwa wasu yankunan masu fama da rikici kamar Liptako Gourma da kuma jihohin Tillaberi da Tahoua da ma a yankunan Agadez da Maradi."

Karin Bayani: Yawaitar yunwa saboda ta'addanci a yankin Sahel 

A tsawon yinin biyu dai, mahalarta taron za su yi musayar bayanai kafin daga bisani su fitar da shawarwari na hanyoyin da ya kamata a bi wajen shawo kan matsalolin tsaro da na zamantakewa a yankunan biyu na Sahel da Tafkin Chadi.