1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kai hari kan sojin Nijar

Salissou Boukari
December 27, 2019

'Yan Nijar na bayyana ra'ayinsu game da sabon harin da aka kai wa sojojin kasar masu rakiyar jami'an hukumar zabe da ke aikin kidaya a yankin Saman a wannan makon da ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaron.

https://p.dw.com/p/3VOMl
Niamey Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Petesch

Wannan sabon hari na zuwa ne makonni biyu bayan da wani harin da 'yan ta'adda suka kai a Inates da ya rutsa da rayukan sojojin kasar sama da 70.

Harin dai ya wakana ne tun a yammacin ranar Laraba da wajejen karfe uku zuwa hudu na yammaci acewar sanarwar hadin gwiwa da ta fito daga ministocin cikin gida da na tsaron kasa, inda suka jaddada mutuwar jami'an tsaron 14 yayin da suka ce daya ya bace.

Wata majiyar ta ce 'yan ta'addan sun kai harin ga ayarin motoci biyar, hudu na jami'an tsaro guda kuma ta ma'aikatan hukumar zabe masu kidayar jama'a, inda suka buda wuta ga motocin biyu na farko da ke bai wa jami'an hukumar zaben kariya.

Sannan daga bisani motoci biyu na jami'an tsaron na Nijar da ke baya, suka fafata da ‘yan maharan da suka yi musu kwanton bauna. Ko da yake wata majiya da ba ta gwamnati ba, ta ce ‘yan ta'addan da yawansu ya kai kimanin 70 bisa babura, sun tafi da mota guda ta jami'an tsaro wadda ake ganin kamar a cikinta ne suka kwashi gawarwakin mutanensu.

Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey - Mahamadou Issoufou
Hoto: AFP/I Sanogo

Ganin cewa wannan hari ya rutsa ga ma'aikatan da ke kidayar masu zabe, tuni wasu suka soma aza ayar tambaya kan shi kanshi batun zaben na jamhuriyr ta Nijar idan iri-irin haka na faruwa

A baya dai gamayyar kungiyoyin fararen hula sun yi kira ga ‘yan kasa da su fito a ranar Lahadi domin nuna goyon baya ga jami'an tsaron na Nijar. Sai dai a Yamai ma'aikatar magajin garin ta ce, ta hana wannan zanga-zanga bisa wasu dalillai, hanin da tuni ‘yan kungiyoyin suka kai karansa a gaban kuliya.

Wannan lamari dai na hare-hare da ke hallaka rayukan sojojin na Nijar ya tayar da hankalin kowa, inda daga nasu bangare su ma malamai suka yi kira da a yi addu'o'i, sannan kowa ya kasance mai yin adalci a cikin tafiya ta kasa:

Yanzu dai bayan wannan hari kallo kuma ya koma ga hukumomi kasar ta Nijar domin aga matakan da zasu dauka, sannan ga batun zanga-zangar ta ranar Lahadi da ake ganin taci ko bata ci ba.