1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashin Nijar da ke samar da ruwan sha

Abdoulaye Mamane Amadou/ MABJuly 13, 2016

Wani matashi kuma shugaban wata kungiya ta farar hula ya tashi haikan a Jamhuriyar NIjar wajen ganin an samar wa al’ummar ruwan sha a ko ina cikin fadin kasar.

https://p.dw.com/p/1JOAn
Zimbabwe Afrika Armut
Hoto: AP

Ousmane Dan Badji mai shekaru 38 a duniya kuma cikakken dan jarida ya jingine aikinsa na rediyo don rungumar wata matsalar da ke addabar galibin alummar Nijar ta samun wadataccen ruwan sha.

Duk da alkawura da hukumomi suka sha yi, sama da kashi 18 % na al'umma na fuskantar karamcin ruwan sha a manyan birane ciki har da Niamey, yayin da wasu kashi sama da 50% na mazauna karkara ke dandana kudarsu a saboda matsalar.

Zimbabwe Afrika Armut
Rashin ruwan sha na hadassa cututtuka a AfirkaHoto: AP

Dabaga na daya daga cikin garuruwan da suka ci moriyar kokuwar dan gwagwarmayar wanda sakamakon matsin lambarsa ga hukumomi, aka kafa wani bututun bayar da ruwan sha kyauta ga mazauna garin. Matasan kauyen suka ce sun gamsu da aikin da Ousmane yake gudanarwa.

Gwamatin dai tace tana saka makuddan kudade da suka kai sama da miliyan dubu 500 a tsawon shekaru 5 da suka gabata don kyautata samar wa jamaa ruwan sha musaman ma mazauna karkara. Sai dai Ousmane Dan Badji ya ce basa samun cikakken hadin kai da taimako daga gwamnati, abubuwan da ke haifar da tarnaki ga gwawarmayar tasu.