1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar bazuwar makamai a yankin tafkin Chadi

Muhammad Bello ZMA
March 24, 2023

Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa a kan yaduwar kananan makamai a tsakanin jama'a ganin yadda hakan ya ke da illa musamman ga mata da kananan yara.

https://p.dw.com/p/4PEHz
UN Vernichtung von Schusswaffen
Hoto: Getty Images/AFP/C. Bouroncle

Bijiro da wannan batu dai a wani taron kasashen da ke makwabtar tabkin Chadi, ya dada haskaka yadda kasashen ke fama da wannan matsala ta bazuwar makamai.

Bayanin bazuwar ta makaman ya fito ne yayin wani taron tattaunawa a kasar tsakanin wakilan kasahen da ke makwabtar tafkin Chadi, wato su Kamaru da Chadi da Nijar. Inda kuma jimlar tattaunawar ta bayyana cewar bazuwar makaman kusan koina ne a wadannan kasashe.

Sai dai kuma Najeriyar bisa la'akkari da yadda matsalolin tsaro su ka yi mata katutu, kamar ta fi bayyana babban hadarin da ta ke fuskanta. gararin bazuwa tare da kasancewar makaman hannayen jamaa a tsukin wadannan kasashe an nunar ya fi ritsawa da mata da kananan yara.

Wata Rakiya Okiri, mazauniyar birnin Fatakwal ce, kuma a satin da ya gabata, ta koka kan yadda Yan bunduga da ke dauke da makamai ke addabar jamaa da ba su ji ba ba su gani ba a birnin na Fatakwal a Jahar Rivers.

"Mu na so hukumomi su tashi haikan kan shawo kan matsalar Yan bunduga da ke hana mu sakat a kusufa kusufa na Birnin Fatakwal, dan a gaskiya su na hana mu sakewa."

Sai dai kan ankararwar da Najeriyar ta yi na cewar makamai su na dada yawaita a hannayen jamaa a kasar da ma kasashen na kewayen tafkin chadi din, na tuntubi wani kwararre kan harkar tsaro a kasar, wani Dakta Uzoma Kingsley, kuma ga abin da ya ke cewa.

"Bullar 'yan tada kayar baya a tsukin kasashen Libya da Misra, kuma musamman ma Libya daga bisanin hambarar da gwamnatin marigayi Gaddafi, bazuwar makamai ta tsananta,hakan kuma ya sa wadannan makamai sun samu tudadowa cikin kasashen Najeriya da Kamaru da Nijar da Chadi."

Wata Farfesa Mina Obanga, kwararra ce kan sharhi a kan manufofin gwamnatoci, kuma ta ce akwai yiwuwar nuna rashin gamsuwa da tsarin shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar jamaa da hukumomi ke yi, wadda kusan ya haifar da jamaa din da dama mallakar makamai, kuma ko da ba bisa kaida ba.

"Da daman jama'a sun dawo daga rakiyar kokarin da hukumomi ke cewar su na yi wajen kare rayuka da dukiyoyin su, sannan sun dawo daga rakiyar tsarin duk da ke kas na aikin tsaron jamaa din,dan haka wasu da dama ke daukar matakin kare kan su, kuma hakan, na dada rura wutar matsalar ta bazuwar makamai koina, haka zalika, ta wani bangaren, dole a kalli yadda Yan fashi da makami da satar mutane don karbar kudaden fansa da 'yan fashin daji da Fulani makiyaya da dai sauran su, da ke haddasa tashe-tashen hankula a garuruwan jama'a."

Tuni dai kasashen na Najeriya da Kamaru da Nijar da Chadi din su ka aminta da ganin cewar wajibi ne su tashi tsaye wajen tunkarar wannan matsala ta bazuwar makamai, inda ma su ka ayyana fara amfanin da wasu yarjejeniyoyi da su ka ce sun rattabawa hannaye a can baya.

Najeriya dai na ci gaba da fuskantar kalubalen 'yan kungiyar Boko Haram da 'yan fashin daji, da 'yan bindugar Niger Delta ma su fasa bututayen danyen mai su na satar sa, da kuma 'yan rajin kafa kasar Biafra yantacciya, kuma dukkanin su na da dimbin makamai tattare gare su.