1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rufe iyakokin Najeriya ya janyo cikas

Mohammad Nasiru Awal
September 19, 2019

Gwamnatin Najeriya ta ce ta rufe kan iyakokin ne a matsayin mataki na dakile masu fasa kwaurin kayan abinci musamman shinkafa daga kasashe makwabta da ma dalilai na yanayin tsaro.

https://p.dw.com/p/3PsYG
Nigeria Seme Grenze zu Benin
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Matakin rufe kan iyakokin Najeriya da mahukuntan kasar suka yi bisa dalilai na magance fasa kwaurin kayan abinci musamman shinkafa 'yar waje da kuma duba batun tsaro, ya haifar da tsaiko ga harkokin kasuwanci da ma zirga-zirgar jama'a tsakanin Najeriya da kasashe makwabtanta.