1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin ruwa a wasu yankunan Nijar

March 20, 2013

Kafewar rijiyoyi a jihar Tanout ya janyo matsalar ruwan sha musamman ga dabbodi, abunda ya sa suke ƙaura domin samun yanayi mai kyau

https://p.dw.com/p/180zh
Frauen tränken ihre Ziegen an einem Brunnen in der Region Tanout, Provinz Zinder, Niger. Bild: DW/Larwana Hami, 20.03.2013, Region Tanout, Niger
Hoto: DW/Larwana Hami

A wasu garuruwan karkarar jahar Tanout dake a yankin damagaram na Jamhuriyar Niger rijiyoyin da makiyaya ke amfani da su wajen baruwan dubunnan dabobi ne suka kama hanyar kafewa, kafewar rijiyoyin dai ta fara tsananta a farkon watan maris wacce ta tilasta ma makiyayan canja ma dabobi lokutan shan ruwa, inda aka fara masu fwashi na kwanaki biyu.

Wanan aiki na baruwan dabobi dai maza magidanta ne aka sani da shi, to sai gashi a yanzu ya komo a hanun 'ya'ya mata, lamarin da ya tura su cin karo da tarin matsalaoli.

Wannan shine karan cakarkara ko kuma elawa inda matan makiyayan ke amfani da dabbobi domin jawo ruwa wanda suke kwashe tsawon yini kafin su sallami bisashe, matsalar kafewar rijiyoyi a jahar Tanout dai ta shafi rijiyoyin Zalalaini, Dingijani, Ano, Ahmet, Intrikten da kuma rijiyar Tenhiya, inda alƙalumma suka nuna a zahiri yadda matan makiyaya ke kara kaina wajen neman ruwa.

A cewar Aishatu Alhusseini da kuma Hadiza a yanzu sun kama hanyar shiga halin tsaka mai wuya babu ruwa, rijiya guda ce kasan lokacin ranin nan matsala kama mutane ya kashe baka da ruwa ka gyara abinci yaranke yana matsala ruwa ne maza sun bar mutane kawkawa da yara rijiya tamu ta garagajiya ruwa sun tone ta sun tone ta duka ta kusa rumjewa mutane sunki shiga balle su yasata in ka tahi da safe sai kazo sha biyun dare da itatuwa mutane suke sarowa manya su zo su gyara,suyi aikin gargajiya

Esel werden getränkt - in der Region Tanout, Provinz Zinder, Niger. Bild: DW/Larwana Hami, 20.03.2013, Region Tanout, Niger
Dabbobi na neman ruwaHoto: DW/Larwana Hami

 Yadda gwamnati za ta taimakawa Tanout

Yau babu abun da ya kamata gwamnati ta kula da mu muma ta mumu gudunmawa yanzu miliyon shidda suka ce gyaranta, yau talaka ka ɗora mishi miliyon shidda yaushe zai hudoshi kulum dai aikin mu kawai na baruwa Allah dai ya kiyaye kawai.

A cewar Ahamet Agirmet da kuma Ihiri daya dayar rijiyar da suka gada daga iyaye da kakanni a hau rijiyar karfe shida mutane da dabobi har zuwa biyar kolfewatake nan da nan shi ne abu wallahi ya ci mumu tuwo a kwariya ta lalace ta bunne bamu da karfin da zamu gyarata mu yasheta rashin ruwa dai yanzu nan ya damemu, tsohuwar rijiyar ya lalace muna ta neman gyaran shi ma kudin sun fi karfin mu a nan zaman da muke dabobi kwana biyu basu sha ruwa ba babbar matsala ce dole zamu gudu mana, yo mutum ya zamna ƙishiriwa ya kashe shi ba ya yuwa..

Nomaden an einem Brunnen in der Region Tanout, Provinz Zinder, Niger. Bild: DW/Larwana Hami, 20.03.2013, Region Tanout, Niger
Makiyaya da dabbobinsu na tafiya mai nesa don samun ruwaHoto: DW/Larwana Hami

Martanin Mahukunta

To ko magabatan jahar ta Tanout suna da labarin wanan matsala ta ruwa na tuntubi magajin garin tenhiya gissa mohamet inda ya fara da cewa lalle akwai matsala tunda mutane ƙaruwa suke rijiya ta gwamnati in an yita ba a kulawa da ita abun dake kaisu kenan suna yin rijiyoyi nasu na kansu in akwai rijiya ta gwamnati sai a samu waɗansu mutane ko wani "shef de tribu" ne su mallaketa su hana ma sauran suce ai wagga rijiya mu aka kawo ma ita ko ko mukayi shi ya sa ake samun matsalar ruwa. waɗansu mutanan sai kaga suna kusa da rijiya gwamnati amma basu iya zuwa sai sun tahi wani wuri nesa.

Wannan wahahalun baruwan dabobi dai yafi tsanani ne a bangaren matan da mazajen makiyaya su suka tafi yawon tabirada zuwa wasu kasashe da suka haɗa da najeriya da kuma kasar libiya larwana malam hami sashen haussa na dw daga rijiyar Intrikten dake cikin jahar Tanout

Mawallafi: Larwana Mallam Hami
Edita:        Pinaɗo Abdu Waba