1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe sojojin Mali 24

Abdul-raheem Hassan
November 19, 2019

Akalla sojojin Mali 24 da wasu mayakan da ke da'awar jihadi su 17 sun mutu a wani artabu tsakanin bangarorin biyu a gabashin kasa. Harin ya faru ne yayin da sojojin kasar da na Nijar ke sintiri na hadin gwiwa.

https://p.dw.com/p/3THM9
Mali Angriff auf EU-Ausbildungslager in Bamako
Hoto: picture alliance/AP Photo/B. Ahmed

Rundunar tsaron Mali ta ce harin ya jikkata wasu 29 an kuma kashe maharan da dama tare da kama daruruwansu, harin ya zo ne bayan wasu hare-hare da ya kashe sojojin kasar da dama a farkon wata.

Tun shekarar 2012 arewacin Mali ke fama da barazanar rashin tsaro duk da fafutukar dakarun hadin gwiwa da Faransa ke jagoranta, amma haryanzu kan iyakar Mali da Nijar da Burkina Faso na fama da barazanar 'yan ta'adda.