1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel da shugabannin Sahel sun tattauna kan tsaro

Mouhamadou Awal Balarabe
May 1, 2019

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na ziyarar aiki a wasu kasahsen Sahel uku ciki har da Burkina Faso da Nijar domin nazarin rawar da rundunar G5 sahel ke takawa wajen magance matsalar tsaro da ake fuskanta a yankin.

https://p.dw.com/p/3HmV1
Deutschland Berlin - Angela Merkel und Roch Marc Christian Kabore
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Sohn

 

Jamus da ma sauran kasashen Kungiyar Tarayyar Turai na sahun gaba wajen taimaka wa rundunar G5 Sahel da ta kunshi sojoji 5000.
Saboda haka ne Christoph Kannengießer, shugaban gamayyar da ke tattare 'yan kasuwan Jamus da Afirka, Afrika-Verein ya ce ziyayar Merkel a yankin Sahel na da matukar muhimmanci.

Ya ce "Ziyarar shugabar gwamnatin Jamus ta kasance babbar alama ta goyan bayan kasashe G5 Sahel, kuma wannan abu ne da shugabannin kasashen ke murna da shi. Jamus tana taimakawa tun shekaru masu yawa da kudi da kayan aiki a yankin. Na yarda da cewa ayyuka na gajeren lokaci bai isa ba, amma wadanda za a dade a na yi sun fi dacewa. "

A lokacin da aka kirkiro da rundunar G5 Sahel a shekara ta 2014, kasashen Burkina Faso, Mali, Mauritania, Nijar da Chadi sun sha alwashin gudu tare don tsira tare daga barazanar tsaro da suke fuskanta. Sai dai shekaru biyar bayan kafata har yanzu rundunar ta kasa sauke nauyin da aka aza mata na kawo karshen hare-haren ta'addanci da ke addabar yankin sahel.  Maimakon haka ma, matsalar tsaro na neman gagarar kundila, inda a baya-bayannan ma aka yi wa Fulani makiyaya kisan gilla a garin Ogossagou na Mali . Amma Thomas Schiller, Darekta reshen gidauniyar Konrad adenauer a birnin Bamako na kasar Mali, ya yi imanin cewa wannan rundunar hadin gwiwar ce  kawai mafita ga matsalar tsaro a kasashen Sahel.

Sahel Konflikt - Malische Armee
Hoto: Getty Images/AFP/D. Benoit

Ya ce "Tabbas ci gaban ba shi da yawa, amma dole a yi la'akari da cewa ba jima da kafa G5 sahel ba.  Kada a yi saurin jiran sakamako ga sabuwar hukuma da ya kamata a tsarata tun daga tushe. Hasali ma ba tara fara aikinta gadan-gadan ba, amma akwai alamun da ke nuna jajircewa na shugabannin kasashen yankin."

Von der Leyen reist in den Niger
Hoto: Picture-alliance/dpa/B. Pedersen

 Ita dai Burkina Faso ta shafe shekaru hudu na baya-bayannan tana fama da hare-hare daga kungiyoyi da ke tsaurin kishi addini dabam-daban ciki har da Ansarul-Islam. Sai dai dakarun rundunar G5 Sahel sun kasa shawo kan tabarbarwar lamarun tsaro da ake fuskanta a Burkina Faso har ma da tsakiyar Mali, inda ake fama da rikicin kabilanci gami da hare-haren ta'addanci.