1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayelsa: Zaben mutum ba jam'iyya ba

Muhammad Bello AH
November 20, 2019

Wani batu da ya dauki hankali a jihar Bayelsa da ke Najeriya shi ne na juyin juya halin siyasar da ya faru, inda al'ummar jihar da PDP ke da karfi suka ki zabar dan takarar da ta tsayar suka zabi jam'iyyar adawa ta APC.

https://p.dw.com/p/3TNnC
Nigeria Symbolbild Wahl
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Sunday Alamba

Da daman jama'a dai musamman wadanda ke wajen Bayelsa na ta mamakin yadda al'ummar Bayelsa suka juyawa jam'iyyar PDP da ke da karfi a jihar baya. Wani bincike na musamman kan jin ra'ayin jama'a game da wannan sauyin matsayi na siyasa, ya gano cewar al'ummar ta Bayelsa sun zabi dan takarar kujerar gwamna na jihar,daga jam'iyyar APC David Lyon saboda irin tallafin da yake bai wa al'ummar jihar.

Siyasar Jihar Bayelsa ta koma ta bin abin da jiha ke cin moriya

Nigeria Lagos - Wahlkampf: Wählerkarten
Hoto: DW/K. Gänsler

Al'ummar Jihar ta Bayelsa na ganin an wuce lokacin bin tsarin kadawa dan takarar jam'iyya kuri'a a zabe idan har ba zai iya kawo sauyi ba ga rayuwar al'ummar jihar. Don haka har kara su zabi wanda ba dan jam'iyyar ba idan yana taimako wajen ci gaban jihar. Mista Amos wani mazaunin Jihar ne ta Bayelsa. Ya ce: ''Na zabi David Lyon na jam'iyyar APC amma hakan ba yana nufin na zabi APC ba ne, saboda David mutum ne da zai iya yin abin kirki a matsayin gwamna, kuma idan aka duba a baya mutum ne da ya ba da kulawa ga matasa na Jihar ta Bayelsa.''

Al'ummar Jihar Bayelsar sun sha alwashin zaben wanda zai tamaki jihar

Jama'ar sun yi ta yin shagulgula inda suka rika furta kalamun cewar daga yanzu idan har jam'iyyar da suke ra'ayi ta PDP ba ta tsaida musu ba, da dan takara na gari ba, za su zabi wanda suka gani zai iya yin aiki mai kyau, ko da ba dan jam'iyyar PDP ne ba.

Nigeria Präsidentschaftswahlen Schlange vor Wahllokal
Hoto: Getty Images/AFP/L. Tato

 

 Eric  Eweke wani dan jarida da kan yi sharhi kan al'ammura na siyasa a Bayelsa

Ya ce: ''  'Yan Bayelsa sun fahimci cewar mutumin da zai kawo musu sauyi ga irin matsalolin da jihar ke fuskanta shi ya dace da su. Kuma mutumin da ya ci gwamna na Jam'iyyar APC a jIhar,mutum ne da ya fahimci matsalolin jama'a.''

 

Yanzu haka  dai akwai bayyanai da ke nuna cewar, jam'iyyar ta PDP a Bayelsa ta yanke kauna ga tsohon shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan, bisa zargin cewar shi ne dalilin rishin samun nasarar jam'iyyar ta PDP a Jihar ta Bayelsa.