1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya da Nijar da Chadi sun ga ta-kai a 2018

Yusuf Bala Nayaya
January 3, 2019

Najeriya ta ga koma bayan fanninta na siyasa da koma bayan tsaro haka ma Chadi yayin da Nijar ta ga koma baya a fanninta na tsaro da ma gwagwarmaya tsakanin 'yan adawa da masu mulki baya ga 'yan kungiyoyin farar hula.

https://p.dw.com/p/3Aykz
Nigeria Tschadsee Konferenz
Hoto: State House, Abuja

Masana a fannin siyasa a Najeriya dai na ganin kasar ta samu koma baya a fagen na siyasa yayin da ake ganin jam'iyya mai mulki farin jininta ya ragu haka nan batu na yarfen siyasa ya mamayi kasar. Ita kuwa a Nijar 'yan adawa da masu fafutika ne suka yi ta fafatawa da gwamnati. Kame-kamen mutane ya ta'azzara cikin shekarar 2018 a Chadi.