1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin matakan tsaro a jihar Zamfara Najeriya

August 30, 2021

Matakan sun hada da rufe kasuwannin jihar da hana hawan babura daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe da kuma hana shiga da fita da dabbobi.

https://p.dw.com/p/3zhS1
Nigeria Demonstration gegen Gewalt im Bundesstaat Zamfara
Hoto: DW/Yusuf Ibrahim Jargaba

Gwamnan jihar ta Zamfara Bello Matawalle ya sanar da sabbin matakan kuma ya sha alwashin cewa ba sani ba sabo ga duk wanda ya sabawa matakan.

Al'ummar jihar sun tofa albarkacin bakinsu kamar suna masu nuna goyon bayansu ga wadannan matakai. Bala Yaro daga jihar ta Zamfara ya shaida wa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba cewa "wannan mataki da gwamnatin jihar Zamfara ta dauka na hana sayar da man fetir ga jarkoki da masu motocin golf, da ke zuwa da babban tanki a ciki masu suna yiwa 'yan bindiga safara, wannan mataki yana da kyau, a rika kula da su kuma duk wanda aka kama a yi masa hukunci."

Karin bayani: An yi garkuwa da dalibai a Zamfara

Sai dai Bala Yaro ya ce hana cin kasuwa zai kara jefa talakawa cikin radadin da suke ciki. "Sai dai  gaskiya mun ji dadi sosai saboda dama matakan da ya kamata a ce ya dauka ke nan tun tuni domin assasa tsaro a wannan jiha."

Matsalar rashin tsaro ta mayar da mutane 'yan gudun hijira a jiharsu ta asali
Matsalar rashin tsaro ta mayar da mutane 'yan gudun hijira a jiharsu ta asali Hoto: DW/Y. Ibrahim

Su ma masana tsaro a Niajeriya irin su Manjo-Janar Janaidu Bindawa marabus na da nasu hange kan matakan gwamnatin jihar ta Zamfara.

"Maganar hana hawan babura daga karfe shida zuwa shida ya yi dai-dai. Kuma maganar rufe kasuwa da hana yawo da shanu su ma hakan ya yi, amma dai ina ganin gwamnati ba za ta tsawaita rufe kasuwannin ba."

Gwamnan Matawalle dai ya bukaci al'umma su daure da wadannan matakai saboda an yi su da nufin saukaka masu ne.

"Wannan mataki dola ne gwamnati ta dauke shi saboda idan mutum ya kare idan za a dora shi, dole sai mutum ya ji wuya, sai ya wahala. Mutane ku yi hakuri wannan mataki da muka dauka mun dauke shi ne domin mu kare rayuwarku da kuma dukiyoyinku."

Masana tsaro na ganin idan wadannan matakai da gwamnatin jihar ta Zamfara ta dauka suka yi nasara to sauran jahohi ma na iya koyi.