1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayar da kararrakin zabe Legas da Abuja

October 17, 2023

A wani abu da ke nuna irin jan aikin da ke cikin sashen shari'ar Najeriya, babbar alkalin kotun daukaka kara ta kasar ta umarci dauke shari'un gwamnoni zuwa biranen Abuja da Legas.

https://p.dw.com/p/4XecQ
Najeriya | Zabe | Kotu | Shari'a | Gwamnoni | Abuja | Lagos
Bayan sanar da sakamakon zabe a Najeriya, masu adawa da shi suka garzaya kotuHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Duk da cewar dai an dauki lokaci ana zargin karbar na goro cikin gidan shari'ar Tarayyar Najeriyar, umarnin shugabar kotun daukaka kara ta kasar na neman daga hakarkari dangane da  rawar alkalan a shari'un zaben kasar. Mai shari'a ta umarci daukacin shari'un zaben gwamnonin da ke gundumomin kotuna 20, su koma zuwa Abuja ko kuma birnin Legas ne domin  kaucewa cin-hanci daga bangaren 'yan siyasa. Umarnin dai na zaman tsoron juya akalar shari'un, a banagren gwamnoni da ragowar masu siyasar Najeiryar da ke da dukiya cikin lalita. Tuni dai 'yan adawar Najeriyar, suka fara nuna alamun damuwa cikin tsarin aiken sakon da illar tsarin dimukuradiyyar kasar ke fuskanta yanzu.

Tasirin sauya fasalin kudi kan zaben Najeriya

Illa cikin gidan alkalai ko kuma kokarin adalci na shugabanci ga kasa dai, koma ya zuwa ina komawar shari'un zaben Abuja da kila ma birnin Legas ke iya yi a kokarin sauya da dama, akwai tsoron abun da ke shirin fita cikin shari'un ka iya jefa ayar tambaya a zuciyar miliyoyin 'yan kasar. Auwal Musa Rafsanjani dai na zaman shugaban kungiyar Transparency in Nigeria da ke a kan gaba a cikin yakin hanci, kuma ya ce rawar cikin gidan alkalan na kama da rawa irin ta mayun gado. Koma ya take shirin kayawa a cikin shari'un zaben a lokaci kankane dai Najeriyar a tunanin Barrister Sa'idu Tudun Wada da ke zaman lauya mai zaman kansa cikin kasar, na da bukatar komawa zuwa ga mai duka cikin barazanar da ke zama mai girma.